'Yan Bindiga sun faɗi kuɗin da za a basu  kafin su saki Sarkin Gobir a Sakkwato

'Yan Bindiga sun faɗi kuɗin da za a basu  kafin su saki Sarkin Gobir a Sakkwato


'Yan bindiga da suka sace tsohon sarkin gobir na Sabon Birni wanda aka mayar uban ƙasar Gatawa a yanzu, sun nemi a ba su fansar naira biliyan ɗaya kafin ya samu 'yanci shi da dansa da kanensa.
Basaraken 'yan bindiga sun yi nasarar garkuwa da shi a hanyar kwanar maharba a lokacin da yake dawowa daga Sakkwato a ranar Assabar data gabata.
Wata majiyar ta ce maharan sun tuntubi sakataren Sarkin Gobir na Sabon Birni kan maganar kudin fansar, ba kai matsaya kan abin da za a ba su ba domin kuɗin da suka fadi ya wuce kima.
Shugaban ƙaramar hukumar Sabon Birni Garba Umar Kaba ya ce bai san yawan kuɗin da suka nema ba amma yasan ana magana da Basaraken ba a abin da ya same shi da dansa da kanensa.
Dan majalisa mai wakiltar Sabon Birni ta Kudu Honarabul Aminu Mustafa Boza ya tabbatar da 'yan bindigar sun nemi kudin fansa, ana kan magana ba akai matsaya ba.
Boza ya bayyana lamarin ya yi ƙamari ba kyau yanda mutane ba su tsira ba a gefensu da makwabtan su a ƙaramar hukumar Isa.