Tambuwal Zai Karbo Bashin Biliyan Hudu Domin Rabawa Manoma a Sakkwato

Tambuwal Zai Karbo Bashin Biliyan Hudu Domin Rabawa Manoma a Sakkwato

 

Tambuwal Zai Karbo Bashin Biliyan Hudu Domin Rabawa Manoma a Sakkwato


Gwamnatin jihar Sakkwato nan ba da jimawa za ta karbo bashin naira biliyan hudu daga tsarin bayar da rance ga manoma na babban bankin kasa CBN ta hannun bankin Zenith domin rabawa manoman jiha.

A zaman majalisar zartarwa da ya gudana ranar Litinin wanda Mataimakin gwamna Manir Muhammad Dan'iya ya jagoranta ne aka aminta da karbo bashin a cewar Kwamishinan kula da lafiyar dabbobi da kiyon kifi kuma mai duba ma'aikatar gona ta jiha Farfesa Abdulkadir Usman Junaidu, manoma dubu 16 da 876 ne za su amfana da bashin.
Ya ce mafiyawan manoman karkara ne za su amfana da bashin, haka ma matsakaitan manoma 732 da manya 180 za su amfana.
Bashin yana da manufar bunkasa noman shinkafa da Alkama da Tumatur, gwamnati za ta kafa kwamitin shawara da masana suka aminta da za  su bibiya lamarin. a cewar Kawamishina.
Ya tabbatar da za su bi yanda doka ta tanadar ga duk wanda zai karbi bashin na sayo kayan aiki da Takin zamani da iraruwa da mashinan aiki.