Daga Abbakar Aleeyu Anache,
Shugaban karamar hukumar mulki ta Zuru a jihar kebbi, Honarabul Bala Mohammed Isah Gajere, yayi Allah wadai da kisan ‘yan Sa-kai 63 Wadanda hare-haren ‘yan ta’adda ya rutsa da su abin da ya yi sanadiyar rasa rayukkansu.
Honarabul Bala Mohammed ya bayyana matukar bakin cikinsa kan abin da ‘yan bindiga suka yi wa mutanen a bata kashin da aka yi tsakaninsu, ‘yan bindigar ne suka yi musu kwanton bauna a wani sabon harin da suka kaddamar, a Dirin Daji.
‘Mutuwar ‘yan Sa-kan wani sabon babi ne a cikin matsalolin tsaro da ake fuskanta’, inji Bala Gajere,
Ya kara jaddada cewa ‘na yi bakin cikin rashin kwamandojin mu da sauran wadanda tashin hankalin ya rutsa da su kuma ina rokon al’ummar Zuru da su taimaki hukumomin tsaro da bayyanan sirri domin samun zakulo da gurfanar da wadannan gungun ‘yan ta’adda a gaban shari’a.’
Shugaban karamar hukumar ya ce bayyanan sirri na dan adam nada muhimmanci a kokarin samun cimma nasara akan wadannan batagari da masu aiki a matsayin masu kwarmata bayanai da hada baki da bata garin suna ruguza zaman lafiyar garuruwansu don neman dan wani ladan kudi da bai taka kara ya karya ba.
Isah Gajere yayi addu’o’in Allah mai girma ya jikan marigayan ya kuma ba al’ummar Zuru hakurin wannan babban rashin da kuma iyalinsu da jure wannan rashi mai zafi sosai.





