Wike zai fasa ƙwai kan rikicinsa da Atiku da rigingimun PDP
Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers Ribas ya ce nan ba da jimawa ba zai “fasa ƙwai” kan abubuwan da ke faruwa a tsakanin sa da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyar PDP, da ma rikicin jamiyyar gana ɗaya.
Wike ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da Kelvin Ebiri, mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai ya sanya wa hannu a biya Asabar a Fatakwal.
Wike ya ce ya dace ya shaida wa ƴan ƙasa kan duk wani abu da ya faru a jam’iyyar, tun bayan samun takara da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi a jam’iyyar.
A cewarsa, “Akan Atiku, zan yi magana nan ba da jimawa ba, kuma ‘yan Nijeriya za su san gaskiyar duk abin da ya faru a PDP a ‘yan kwanakin nan."
managarciya