Jam'iyyar PDP A Zamfara Ta Koka Kan Shirin  Hanasu Buda Sakatariya

A cewar Shatiman Rijiya bayan an kwace masu wannan wurin sai suka kara gaba suka samu wani wuri domin buda wani ofis amma duk da haka sai suka kara komawa wannan sabon wurin suka yi masa fentin APC suka goge wanda PDP ta yi, don gudun tashin hankali sai suka yi  shiru basu  ce komai ba. "Yanzu kuma mun dauki hayar wani wuri a shiyar Samaru dake nan Gusau, akan kudi naira miliyan goma ga shekara, kuma  kafin mu fara gyaran wurin mun bada takar dar neman izinin bude sakariyar mu ga hukumar tsara birnin Zamfara, amma har tsawon wata daya basu bamu amsa ba.

Jam'iyyar PDP A Zamfara Ta Koka Kan Shirin  Hanasu Buda Sakatariya

Jam'iyyar PDP jihar zamfara ta koka kan bita da kullin da akeyi masu tun lokacin da suka raba gari da wayan su yayan jam'iyyar.

Mukaddashin sakataren watsa labarai na PDP Alhaji Faruku Ahmad Gusau, Shatiman Rijiya ya yi wannan koken a lokacin da ya kira  taron manema labarai na gaggawa a sakatariyar su dake garin Gusau babban birnin jiha.

Yace tun lokacin da wasu daga cikin su suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, suka kwace masu babbar sakatariya suka mayar da ita ta tasu.

A cewar Shatiman Rijiya bayan an kwace masu wannan wurin sai suka kara gaba suka samu wani wuri domin buda wani ofis amma duk da haka sai suka kara komawa wannan sabon wurin suka yi masa fentin APC suka goge wanda PDP ta yi, don gudun tashin hankali sai suka yi  shiru basu  ce komai ba.

"Yanzu kuma mun dauki hayar wani wuri a shiyar Samaru dake nan Gusau, akan kudi naira miliyan goma ga shekara, kuma  kafin mu fara gyaran wurin mun bada takar dar neman izinin bude sakariyar mu ga hukumar tsara birnin Zamfara, amma har tsawon wata daya basu bamu amsa ba.

" Sai muka ga har sun wuce doka mu kuma mu kaci gaba da gyaran wurin, kwatsam sai hukumar ta zo tasa muna jan fenti tace wai mu dakata da aikin da mukeyi, ganin wannan yasa muka tuntubi lauyoyin mu inda suka rubuta ma hukumar takardar gargadin cewa za' aci gaba da aikin gyaran sakatariyar, amma dai sunki su bamu cikakken bayani a hukuman ce.

"Mu kuma muka ci gaba da aikin mu, sai gashi kwatsam sun kara dawowa domin hanamu aikin, mu mutane ne masu bin doka da oda kuma masu son zama lafiya saboda haka shi yasa muka kira ku domin mu fada maku irin bita da kullin da hukumar tsara birnin Zamfara keyi muna." Inji Shatiman.

Alhaji Faruku ya kara da cewa, yaji ance wai wurin da suka kama hayar na kasuwan cine, adon haka bai kamata ace anyi ofishin siyasa a wurin ba, daga nan sai yace dokar kasa ta basu damar buda ofishin jam'iyya tun daga mazaba har zuwa jihar, kuma siyasa ai kasuwanci ce.

Ya kara da cewa ko lokacin mulkin tsohon gwamna Alhaji Abdul Aziz yari Abubakar inda suka yi adawar siyasa mai zafin gaske  ba'a taba hanasu buda ofishin siyasa ba, kuma shi gwamnan na yanzu yasan da hakan.

"Muna kara kira ga magoya bayan mu da su yi hakuri, domin komi yayi farko zaiyi karshe, kuma muna nan muna tattara irin barnar da akayi muna domin daukar matakin da ya dace, haka zalika muna nan muna tattaunawa da lauyoyin mu domin su bamu shawarwarin da zamu bi.inji shi.

Daga Aminu Abdullahi Gusau.