2023: Jam'iyyar APC ta karbi karin masu sauya sheka a Sokoto

2023: Jam'iyyar APC ta karbi karin masu sauya sheka a Sokoto

 

Jam'iyyar APC, mai adawa a jihar Sokoto, tace ta karbi karin wasu masu sauya sheka daga jam'iyyar PDP da sauran jam'iyyu zuwa jam'iyyarta a jihar. 

Wannan na kunshe ne cikin wata takarda da mai taimakawa tsohon gwamna jihar ya rabawa manema labarai a Jumu'a a Sokoto. 
A cewar sanarwar dubban masu sauyin shekar sun fito ne daga yankuna Gwadadawa, da Wamakko da sauran kananan hukumomi.
“Wanda suka sauya shekar sun hada da tsoffin kansiloli, da masu rike da mukamai a jam;iyyar da suka baro". 
“Gaba daya wanda suka sauya shekar sun sami tarba tun daga matakin karamar hukumarsu da kuma tarba ta musamman daga dan takarar gwamna jihar da mataimakinsa,”.  
Sanarwar ta kara da cewa sauyin shekar zai baiwa jam'iyyar kwarin gwuiwa da fatan samun nasara a zaben shekarar 2023.
Da yake jawabi a wajen taron, Maigari Dingyadi, ministan harkokin ‘Yan sanda, ya bayyana ci gaban a matsayin nasara, bayan nasarorin da gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC ta samu. 
“Gwamnatin APC karkashin kulawa shugaba Muhammadu Buhari ta kawo ayyukan ga kasa masu inganci da nufin yin tasiri ga rayuwar jama’a."