El-Rufai Ya Janye  Sha’awar Zama Ministan Tinubu

El-Rufai Ya Janye  Sha’awar Zama Ministan Tinubu

 

Wani rahoto da Premium Times ta kadaita da shi, ya bayyana cewa Nasir El-Rufai bai sha’awar zama minista a sabuwar gwamnatin tarayya. 

Nasir El-Rufai bai sha’awar yin aiki da Bola Ahmed Tinubu bayan abin da ya faru a wajen tantance wadanda ake so su zama ministoci a kasar nan. 
Da aka yi zama da tsohon gwamnan na jihar Kaduna a makon nan, wasu majiyoyi sun shaida cewa ya fadawa Bola Tinubu bai sha’awar rike mukami. 
Malam Nasir El-Rufai ya nuna zai bada gudumuwarsa wajen gyara kasa a matsayin mai zaman kan shi, ba tare da ya taka rawar gani a gwamnati ba. 
Tsohon ministan ya nunawa shugaba Bola Tinubu cewa ya na bukatar lokaci domin ya maida hankali a kan karatun digir-digir da yake yi a kasar waje. El-Rufai ya na kokarin kammala digirinsa na PhD a wata jami’a da ke kasar Netherlands a Turai.
Rahoton ya ce idan ana bukatar shawararsa a kan wanda zai iya rike kujerar minista a gwamnatin tarayya, El-Rufai ya bada sunan Jafaru Ibrahim Sani. 
Malam Jafaru Ibrahim Sani ya rike matsayin kwamishina a ma’aikatar kananan hukumomi, ilmi da muhalli a lokacin ‘dan siyasar ya na Gwamna. Idan an gagara shawo kan shi, watakila a dauki Jafaru Sani ko wani dabam daga Kaduna domin a samu wanda zai wakilci jihar a majalisar ministoci. 
Da jin labarin jami’an tsaro ba su kai ga yin na’am da nadin shi a matsayin minista ba, El-Rufai ya na dawowa, ya nemi ya zauna da shugaban Najeriya. A lokacin da labarin ya fito, rahoton ya ce Malam ya iso Najeriya daga Landan kenan. 
A wajen zaman ne Bola Tinubu ya fada masa SSS ta aiko korafi game da shi, kuma ana bukatar a duba rahoton, a nan ya nuna bai bukatar wani mukami.