Wike Ya Goyi Bayan Gwamnan Bauchi Ya Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa A 2023

Wike Ya Goyi Bayan Gwamnan Bauchi Ya Tsaya Takarar Shugaban Ƙasa A 2023

Gwamnan Rivers Nyesom Wike, ya ce jam'iyarsa ta PDP matuƙar tana son samun nasara a zaɓen 2023 tau ta tsayar da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad ya yi takara.

Wike ya nuna rashin jin daɗinsa kan rikicin da ke faruwa kan matsalar tsaro don haka lokaci ya yi da PDP za ta dawo don kuɓutar da ƙasa.

Gwamnan a lokacin da yake karɓar amsar tambayoyi ga manema labarai ya ce Allah ba zai yafewa PDP ba matuƙar ba ta cika burin mutanen Nijeriya ba ta dawo kan mulki.

Ya ce yana son wannan shekara ta 2022 tafi wadda ta gabata, haka kuma a tabbatar da PDP ta riƙa tafiya cikin haɗin kai, in PDP ta yi kuskure rashin sauraren mutanen Nijeriya, da wahalar gaske Ubangiji ya yafe masu.