Chukwuemeka Eze, fitaccen jagora a jam'iyyar APC kuma na hannun daman Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri, ya ce a dora wa Bola Tinubu laifi idan Amaechi ya bar jam'iyyar.
Eze yana magana ne kan wani rahoto da ke ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar yana zawarcin Amaechi, The Punch ta rahoto.
Idan za a iya tunawa Eze a baya-bayan nan ya kasance yana magana kan Amaechi kuma ya ce idan Amaechi ya shiga PDP, laifin Tinubu ne, wato dan takarar shugaban kasa na APC.
Ya yi ikirarin cewa a dora wa tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar mai mulki idan tsohon ministan ya fita daga APC.
"Idan Amaechi ya yanke shawarar shiga PDP, ta yi wu ba laifinsa ba ne amma saboda abubuwa da halin Sanata Bola Ahmed Tinubu da masu kula da kamfen dinsa tare da sabbin shugabannin da ke tafiyar da harkokin APC a yanzu," in ji Eze.