Rikici ya kunno kai a NNPP yayin da jam'iyyar ta dakatar da Sakataren Gwamnati da Kwamishina a Kano 

Rikici ya kunno kai a NNPP yayin da jam'iyyar ta dakatar da Sakataren Gwamnati da Kwamishina a Kano 

Jam'iyyar NNPP mai mulki a Jihar Kano na fuskantar sabon rikici yayin da a daren jiya Litinin ta dakatar da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi da Kwamishinan Ma'aikatar Sufuri, Muhammad Diggol.

Rikicin ba zai rasa nasaba da rashin fahimtar juna ba tsakanin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a karamar hukumar Bichi ta jihar.

Shugaban jam'iyyar na jiha Kano,  Hashimu Dungurawa, wanda ya tabbatar da dakatarwar ga manema labarai, ya ce an dakatar da su ne saboda rashin biyayya, zarmewa da kuma kawo hargitsi a cikin jam'iyyar.

A kalamansa, "Mu na sanar da cewa mun dakatar da Sakataren Gwamnati,  Abdullahi Baffa Bichi da Kwamishinan Sufuri, Muhammad Diggol saboda rashin biyayya ga jam’iyya da kuma zagon kasa."

"Muna yabawa shugabannin jam’iyyar daga mazabunsu da karamar hukumar Bichi  da Kano ta Arewa, wadanda suka tabbatar mana da suka kawo batun a rubuce."

Tun da fari, kafin sanar da dakatarwar, Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya shiga tsakani don sasanta masu ruwa da tsaki a cikin NNPP da manyan shugabannin tafiyar Kwankwasiyya a jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature, ya fitar, ya ce nasarar sasantawar da aka yi  a ofishin Gwamnan a ranar Litinin da maraice ta kawo karshen rikicin da ya addabi tsarin cikin gida na jam’iyyar.

Wadanda za a yi wa sulhun sun hada da Sakataren Gwamnatin Jiha, Dr. Abdullahi Baffa Bichi, da dan takarar Shugaban Karamar Hukumar Bichi, Hon. Hamza Sule Maifata.

Da ya ke jawabi ga ‘yan jarida bayan zaman sulhun, Baffa Bichi ya cyi alkawarin warware sabanin sa da kungiyar dake fafutuka a mazabarsa ta Bichi da kungiyoyin da suke sukar sa.

Dr. Bichi ya nesanta kansa daga kungiyar 'Abba Tsaya da Kafar ka' da ke kira da a raba tsakanin Gwamna da shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.