Yadda Ake Haɗa Wainar Fulawa Mai Haɗe Da Garin Banbara

Yadda Ake Haɗa Wainar Fulawa Mai Haɗe Da Garin Banbara

Wainar fulawa mai haɗe da garin banbara

Kayan haɗi;

Fulawa
Banbara
Maggic
Mai
Attarugu
Albasa

Yadda ake haɗawa.

Dafarko ƴar uwa zaki tanadi fulawarki da garin banbara, zaki ɗibi garin banbararki kwatankwacin yadda kike son sa, ki zuba a mazubi me ɗan girma, ki zuba ruwa a ciki ki barshi ya ɗanyi mintuna a cikin ruwan.
Sannan ki ɗauko fulawarki ki nemi mazubi itama ki zuba ta a ciki, saiki ɗauko jiƙaƙƙiyar banbararki ki samu mataci ki tace ta, ki tabbatar baki zuba mata ruwa da yawa ba tun wurin jiƙonta, ta yadda za tayi kauri idan kika tace ta kenan. Ki kwaɓa fulawarki da waɗannan ruwan banbarar taki, idan ruwan be isa ba, ki ƙara ruwan saikin tabbatar kwaɓin ya yi yadda ki ke so. Ki ɗauko attarugunki wanda dama kin jajjagashi a turmi shi da albasa da ƴar tafarnuwa ki zuba a cikin kwaɓinki. Ki saka maggic da gishiri da duk wani sinadarin ɗanɗano dai. Dama kin tanadi wurin da zaki toya wainarki dai, ki nemo murfi ko tanda ki toya wainarki da mai lafiya lau. Zaki ga ta yi santsi da ma'ana gwanin sha'awa. Idan ki kaje wurin ci kuwa, Hajiya zaki bayar da labari. Domin kuwa santsi ne da garɗi zai dinga ratsa kusurwar gangar jikinki.

Aci daɗi lafiya.


DOCTOR MARYAMAH.