Bukin Kirismati:Ba Zan Yi Sanyin Guiwa Ba Wajen Kare Dukiya Da Rayukan Jama'a- Inji Gwamna Neja

Bukin Kirismati:Ba Zan Yi Sanyin Guiwa Ba Wajen Kare Dukiya Da Rayukan Jama'a- Inji Gwamna Neja
Bukin Kirismati:Ba Zan Yi Sanyin Guiwa Ba Wajen Kare Dukiya Da Rayukan Jama'a- Inji Gwamna Neja
Daga Babangida Bisallah, Minna
 Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja kuma shugaban kungiyar gwamnonin arewa ta tsakiya, ya taya mabiya addinin kirista murnar bukin kirismati na shekarar 2021 dan tunawa da haihuwar Jesu Kiristi.
A sakon gwamnan na bukin kirismati, ya janyo hankalin mabiya addinin kirista da su yi anfani da wannan ranar wajen nuna soyayya, kauna, zaman lafiya musamman ganin yanayin da muke bukata ke nan a halin yanzu da muke fama da matsalar tsaro a jiha da kuma wasu sassan kasar nan.
Ya baiwa al'ummar jihar tabbacin cewar gwamnatinsa za ta tabbatar ta kara kaimi wajen tabbatar da tsaro dan samun zaman lafiya da walwalar jama'a a jihar.
Gwamnan yace gwamnatin jihar za ta cigaba da bada goyon baya da gudunmawa da dan abinda ta ke samu ga jami'an tsaro dan kara basu kwarin guiwa na dakile matsalar tsaro.
Gwamnan ya yabawa jami'an tsaro kan yaki da yan ta'adda a jihar, gwamna Sani Bello yace kar su karaya su cigaba har a cin ma nasarar da ake bukata.
Ya janyo hankalin jama'ar jihar da su cigaba da baiwa jami'an tsaro goyon baya, ta hanyar bada sahihan bayanai kan yan ta'adda ko wasu batagari ko wani abinda yake yiwa zaman lafiya barazana a yankunan su dan kawo karshen fakewar batagari a cikin mutanen kirki.
" Na sani samar da tsaro ga al'umma a jihar nan hakki na ne, yana daga cikin kudurin wannan gwamnatin samar da zaman lafiya, walwalar jama'a, kuma zan tabbatar na sauke nauyin da ke kai na.
Ba zan samu natsuwa ba akan rashin kula da hakkin jama'a akai ba, na samar da tsaro rayuka da dukiya ba. Al'ummar mu zasu samu yancin zama duk inda suke bukata dan yin rayuwa ba tare da wata barazana ba, halin da muke cikin a yanzu, zamu tabbatar mun samar da walwala ta yadda tattalin arziki zai bunkasa dan samun tsayayyen walwala ga yan kasa".
Gwamnan yayi addu'ar yayi addu'ar nasarar shiga shekarar 2022 ga dukkan al'ummar jihar.