Tinubu zai rantsar da sabuwar Alƙalin Alƙalan Nijeriya 

Tinubu zai rantsar da sabuwar Alƙalin Alƙalan Nijeriya 

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, zai rantsar da Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun a gobe Juma'a a matsayin babbar Alƙalin alƙalan ƙasar don maye gurbin Olukayode Ariwoola da ya yi ritaya a ranar Alhamis.

Cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar kan kafofin yaɗa labarai, Dada Olusegun ya wallafa a shafinsa na X, ya ce shugaban zai rantsar da Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin Alƙalin Alkƙalan Najeriya ta 23 a ranar Juma'a.

Za a gudanar da bikin rantsarwa a Abuja fadar gwamnatin ƙasar, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

A ranar Alhamis ne Mai Shari'a Olukayode Ariwoola ya yi ritaya bayan cika shekara 70 da haihuwa.

Mista Ariwoola ya yi aiki a fannin shari'ar ƙasar inda ya riƙe muƙamai daban-daban, kafin ya kai ƙololuwa a fannin