Matasa Na Kokarin Hana Rashawa sai Dai----Hajiya Ubaida Muhammad Bello

Matasa Na Kokarin Hana Rashawa sai Dai----Hajiya Ubaida Muhammad Bello

 

Kungiyar Africmil da hadin guiwar gidauniyar Hcomdi sun shirya taron wayar da kai na yini daya kan amfanin da kwarmato yake da shi a wurin yakar rashawa a Nijeriya.

Hajiya Ubaida Muhammad Bello Sarauniyar Sharifai shugabar Hcomdi ta bayyana cewa sun kira masu ruwa da tsaki ne don samar da tsarin da zai kare masu kwarmaton cin hanci da rashawa a Nijeriya.
Hajiya Ubaida ta ce sun ga da cewar zama da kungiyoyi masu zaman kansu guda 40 tare da hukumar EFCC da ICPC da NOA don sanar da su tanadin da kungiyoyin kasashen waje suka yi ga masu kwarmato.
Sarauniyar Sharifai a bayaninta ta ce matasanmu na kokari wurin hana rashawa sai dai rashin kariya na hana masu kwarmato "a wannan zaman za su San kariyar da suke da ita da doka ta aminta da yanda za a bi cikin hikima. Muna shiri na musamman domin kai ziyara majalisar dokoki don koka masu da neman samar da doka da amfani da ita.
"Kuma za mu ilmantar da mutane su San bambancin kwarmato da tsegumi don wasu na ganin daya ne, tsegumi abu ne da baya da amfani,,  kwarmato za a kai shi ne in da zai yi amfani a walwale matsala a dakile wani sha'ani da ake kullawa da zai gurgunta kasa," a cewar Ubaida.