Tambuwal ya sake mayar da albashin kananan kananan ma'aikata a kananan hukumominsu

Tambuwal ya sake mayar da albashin kananan kananan ma'aikata a kananan hukumominsu

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya amince da mayar da ma’aikatan kananan hukumomi albashin kananan hukumomi zuwa kananan hukumominsu.

 
 Kwamishinan kananan hukumomi da cigaban al’umma na jihar, Alhaji Abdullahi Maigwandu ne ya sanar da hakan a wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar Muhammad Umar Sanyinna.
 
 A cewar sanarwar, kananan ma’aikatan da umarnin ya shafa sun hada da, daga matakin “01” zuwa “06”.
 
 Sai dai kuma ma’aikatar kula da kananan hukumomi da ci gaban al’umma za ta kula da albashin wadanda suka fito daga matakin “07” zuwa sama.
 
Sabon cigaban a cewar Kwamishinan, shi ne karfafa yin aiki a kan lokaci na ma'aikatan kananan hukumomin.
 
 Abdullahi Maigwandu ya yi amfani da kafar sadarwar wajen jaddada kudirin gwamnati mai ci a jihar na tabbatar da jin dadin ma’aikatanta a kowane mataki.
 
Yayin da ya bukaci manyan ma’aikatan kananan hukumomin da su goyi bayan wannan sabon umarnin domin a samu nasara, ya kuma yi kira ga sauran ma’aikatan da su kasance a kan lokaci su ji tsoron Allah wajen sauke nauyin da aka dora musu.