Yan Arewa Ni Suke Bukata, Ba Wani Bayarabe Ko Inyamuri Ba--- Atiku

Yan Arewa Ni Suke Bukata, Ba Wani Bayarabe Ko Inyamuri Ba--- Atiku

Dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa shi yan Arewa ke bukata a 2023 ba dan takara Bayarabe Ko Igbo ba.

Atiku ya bayyana cewa a matsayinsa na dan Arewa, ya shiga kowani lungu da sako na kasar nan kuma ya fahimci ko ina. 
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya bayyana hakan ne yayinda yake amsa tambyar Kakakin kungiyar dattawan Arewa, Hakeem Baba-Ahmed a jihar Kaduna ranar Asabar. 
Kungiyoyin yankin Arewacin Najeriya sun shirya taron tattaunawa da dan takarar a gidan tarihin Arewa House dake jihar Kaduna. 
Kungiyoyin sun hada da Arewa Consultative Forum, Arewa House, Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation, Northern Elders Forum, and Arewa Research and Development Project, dss. 
"Abinda kowani dan Arewa ke bukata shine Dan Arewa kuma wanda ya fahimci kowani sashen kasar nan." 
"Dan Arewa bai bukatar dan takara Yoruba ko Igbo, na cikakken dan Najeriya kuma dan Arewa."