Tinubu Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ya Zaɓi Shugaban INEC

Tinubu Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ya Zaɓi Shugaban INEC

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa dalilin da ya sa ya zabi Farfesa Joash Amupitan (SAN) a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) shi ne saboda amincinsa, rashin nuna bambancin siyasa da kuma kwarewarsa a aikinsa.

Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin taron Majalisar Koli ta Ƙasa da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja, inda mambobin majalisar suka amince da nadin Farfesa Amupitan a matsayin wanda zai maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu, wanda wa’adinsa na shekaru goma ya ƙare a ranar Talata.

A cewar kakakin shugaban ƙasa, Mista Bayo Onanuga, Tinubu ya ce: “Amupitan mutum ne mai gaskiya, ba ya da alaka da kowace jam’iyyar siyasa, kuma shi ne mutum na farko daga Jihar Kogi da aka taɓa naɗa a wannan mukami.”

Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya bayyana cewa tarihin Amupitan ya nuna irin jajircewarsa wajen adalci, ilimi da sadaukarwa ga ƙasa.

Farfesa Amupitan, mai shekaru 58, haifaffen garin Ayetoro Gbede ne a Ƙaramar Hukumar Ijumu ta Jihar Kogi. Yanzu haka shi ne Mataimakin Shugaban Jami’ar Jos (bangaren gudanarwa) kuma Pro-Chancellor na Jami’ar Joseph Ayo Babalola da ke Osun.

Ya karanci dokoki a Jami’ar Jos, inda ya samu digiri na farko, na biyu da na uku a fannin doka. An kira shi zuwa mashaya lauyoyi a shekarar 1988, sannan ya zama Lauya Babba (SAN) a 2014.

Amupitan ya rubuta littattafai da dama a fannin dokar kamfanoni, shaidu da tsarin gudanarwa, kuma ya taba zama memba a hukumomi da dama a Najeriya.

Idan majalisar dattawa ta tabbatar da nadinsa, zai zama Shugaban INEC na 15 a tarihin Najeriya.