Gwamnonin Najeriya sun yi ta'aziyyar rasuwar ƴan Wasan Kano

Gwamnonin Najeriya sun yi ta'aziyyar rasuwar ƴan Wasan Kano

Kungiyar Gwamnonin Najeriya  ta bayyana alhini da jimami kan rasuwar wasu 'yan wasa daga jihar Kano sakamakon mummunan hadarin mota da ya auku a ranar Asabar.

Lamarin ya faru ne a yayin da tawagar 'yan wasan jihar ke dawowa daga gasar wasanni ta kasa da aka kammala kwanan nan a Jihar Ogun.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a yau Asabar.

“Muna mika sakon ta’aziyyarmu  ga iyalan 'yan wasan, gwamnatin jihar, da kuma masu ruwa da tsaki a fannin wasanni a jihar Kano da Najeriya baki daya.

“Muna rokon Allah Ya jikan 'yan wasan da suka rasu, Ya kuma ba iyalansu hakuri da juriyar wannan babban rashin,” in ji AbdulRazaq.