Shahrarren Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi kira ga Hukumar tsarin farin kaya, DSS, ta gaggauta sakin Tukur Mamu ko ta kai shi kotu. Gumi ya bayyanawa gwamnati cewa dokar kasa bata amince a rike mutum sama da kwana guda ba'a kai shi kotu ba.
A zaman karatun littafin Muktasarul-Khalil da Malamin ke yi mako-mako a Masallacin Sultan Bello dake Kaduna, Gumi yace wannan jarabawa ce ga Tukur Mamu kuma Allah ya sa yaci jarabawar.
"Na san sharrin Security (jami'an tsaro), domin (shin) Sardauna ya tsira daga sharrin Security (jami'an tsaro), Murtala ya tsira daga sharrin Security (jami'an tsaro), Maimalari ya tsira daga sharrin Security (jami'an tsaro), IBB ya tsira daga sharrrin Security, shi kanshi Buharin ya tsira daga sharrin Security (jami'an tsaro)?."
"Ni na san abinda ku baku sani ba. Ni shawara nike bawa hukuma ta sakeshi a mance da lamarin mu roke shi yayi hakuri."
"Muna kira ga hukumar tayi mishi adalci, kundin tsarin mulkin kasa yace kada ka kama mutum sai ka samu hujja wanda gobe-gobe zaka kaishi kotu, kuma in kun samu hujja mara karfi sosai ku kai kotu sai kotu tace a cigaba da rikeshi, shine doka.
"Muna yaki da yan ta'adda saboda basa bin doka, Idan gwamnati bata bin doka kuma tana rike da makami itama ta zama yar ta'adda, me banbancinsu?"