Zaɓen ƙananan hukumin Sakkwato: APC a Tambuwal ta kasa cimma matsaya

Zaɓen ƙananan hukumin Sakkwato: APC a Tambuwal ta kasa cimma matsaya

Zaɓen ƙananan hukumin Sakkwato: APC a Tambuwal ta kasa cimma matsaya

 
Jam'iyar APC a jihar Sakkwato ta bi sahun sauran jhihohin Nijeriya wurin gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomin jihar 23.
Jam'iyar APC a jihar ta aminta da a yi zabe ba mahayya a ko'ina cikin jihar kuma haka aka yi a kananan hukumomi 22 in ba da Tambuwal da aka samu masu yin takarar shugaban jam'iya a karamar hukumar su biyu Alhaji Abubakar Muhammad  Babba,da wanda shi ne ya sauka a rikon kwarya  Alhaji Ummaru Maitafsir.

Shugaban kwamitin gudanar da zabe a karamar hukumar Honarabul Malami Muhammad Galadanchi wanda aka fi sani da Bajare ya ce sun yi zabe ba hamayya a sauran mukaman shugabanci 26 da daligate na kasa guda uku, kujerar ciyaman ce kawai ke da hamayya, in da mutum biyu ke takara.
"An samu wasu matsaloli ne da suka hana kammala zaben a yau(Assabar) muka dage sai gobe(Lahadi), mun sanar da uwar jam'iya kuma ta shiga lamarin a gyara matsalolin gobe za mu zo ne a yi zaben shugaba kawai domin shi ne ya rage ba a yi ba a karamar hukumar Tambuwal." a ceawar Bajare.

A bayanin da Managarciya ke samu an gudanar da zaben lafiya a sauran kananan hukumomin jihar.