Sarkin Sudan Ya Rasu Yana Da Shekara 85 A Duniya

Sarkin Sudan Ya Rasu Yana Da Shekara 85 A Duniya
 

 

Gwamnan jihar Sakkwato a jawabin da ya fitar da kansa ya tabbatar da rasuwar Sarkin Sudan na Wurno Alhaji Shehu Malami a ranar Litinin data gabata.

Gwamnan ya ce ya samu labarin rasuwar daya daga cikin jagorori a daular Usmaniya, da ya bar duniya da shekara 85 gogaggen ma'aikacin banki ne da ke da kwarewa a harkar masana'antu da ke da ta cewa a harkokin Nijeriya.
Alhaji Shehu Malami haifaffen jihar Sakkwato ne da ya yi karatunsa daga Furamare zuwa jami'a a tsakanin garin Bida da Katsina da Landan.
Ya yi zama mataimaki na musamman ga Sarkin musulmi Sadik Abubakar na uku ya yi aiki  da dama da suka shafi tattalin arziki da cigaban kasa ya kuma zama jakadan Nijeriya a kasar Afirika ta Kudu.
Tambuwal a madadin gwamnati da mutanen jihar Sakkwato ya yi ta'aziyar rashin Sarkin Sudan ga mai martaba Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar, Allahi ya jikansa ya gafarta masa ya baiwa iyali da masoya hankurin rashinsa da aka yi.