Tambuwal Na Cikin Hadari: Wa'adin Da Hukuma Ta Ba Shi Ya Cika

Tambuwal Na Cikin Hadari: Wa'adin Da Hukuma Ta Ba Shi Ya Cika
 
Kwamitin neman bayani da gwamnatin Sakkwato karkashin jagorancin Dakta Ahmad Aliyu ta kafa don samar da wasu bayanai kan yadda aka kashe kudin Gidajen gwamnati da sauran bayanai kan filaye ya aminta da bukatar da tsohon Gwamna Aminu Waziri da wasu mutum 9 suka gabatar masa na neman karin lokaci da za su kare kansu, an ba su kwana biyu in da yake cika yau Alhamis.

Kwamitin ya dawo da cigaba da sauraren bayani ga wadanda abin ya shafa a Talata data gabata sun gayyaci Sanata Tambuwal da wasu mukaraban gwamnatinsa matsayin shedu.

Aminiya ta rahoto an gayyaci shedannun ne domin su yi bayanin rawar da suka taka a wurin gwanjo da sayar da kadarorin gwamnati da wasu da suka shafi ma'aikatar gona.

A lokacin sauraren Suleiman Usman lauyan Tambuwal da mutanen 9 ya  nemi a kara masu lokaci domin mayar da  martani kan abin da aka bukace su.

Lauya Usman ya jawo hankalin cewa wasu daga cikin shedu ba a sanar da su yanda yakamata ba kan haka ake bukatar karin lokaci.

Mutanen da ake bukatar su bayyana gaban kwamitin bayan tsohon gwamna Aminu Waziri Tambuwal sun hada da Sani Garba Shuni da Sa'idu Umar da Abdussamad Dasuki da Ali Inname da Aminu Dogondaji da Buhari Tambuwal da Umar Wali da Umar Bature da Mai-Akwai Tudu da Aliyu Tureta da sauransu.

Alkali Mu'azu Pindiga wanda yake shi ne shugaban kwamitin ya amince da rokon da aka yi ya ba su kwana biyu.

A zaman baya da aka yi wasu daga cikin mutane su uku sun aminta su dawo motocin  noma Tarakta da aka yi masu gwanjonta cikin kwana biyu, sun ce motocin an ba su ne domin su yi noman ridi.  

Pindiga ya sanya 5 ga watan Okotoba don soma sauraren mutanen da suka gayyata.

Ana sa ran Sanata Tambuwal ya gurfana gaban kwamitin a yau Alhamis kamar yadda lauyansa ya nema musu karin lokaci don shiryawa.