Siyasa: PDP Da APC Na Zaɓar Shugabanninsu A Jihohi

Tuni APC mai mulki ta bayar da sanarwar dakatar da zaɓen a Jihar Oyo da ke kudancin ƙasar sakamakon abin da ta kira "yunƙurin maguɗi" sannan ta umarci kwamatin shirya zaɓen ya koma sakatariyarta ta ƙasa domin tattaunawa. Rahotanni sun nuna cewa Gwamnan Adamawa Umaru Fintiri da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma jigo a PDP Atiku Abubakar sun kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen da ke gudana a Dandalin Ribadu da ke Yola babban birnin Adamawa.

Siyasa: PDP Da APC Na Zaɓar Shugabanninsu A Jihohi

Daga: Comrade Musa Garba Augie.

Manyan jam'iyyun siyasar Najeriya na APC da PDP na gudanar da zaɓukan fitar da shugabanninsu a matakin jihohi a yau Asabar.

Sai dai PDP mai adawa na gudanar da zaɓukan ne a jiha bakwai kacal - Oyo da Kwara da Legas da Adamawa da Borno da Kebbi da kuma Ebonyi.

Tuni APC mai mulki ta bayar da sanarwar dakatar da zaɓen a Jihar Oyo da ke kudancin ƙasar sakamakon abin da ta kira "yunƙurin maguɗi" sannan ta umarci kwamatin shirya zaɓen ya koma sakatariyarta ta ƙasa domin tattaunawa.

Rahotanni sun nuna cewa Gwamnan Adamawa Umaru Fintiri da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma jigo a PDP Atiku Abubakar sun kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen da ke gudana a Dandalin Ribadu da ke Yola babban birnin Adamawa.

Idan aka kammala, zaɓukan ne za su fitar da shugabannin da za su jagoranci jam'iyyun a matakan yayin da ake tunkarar babban zaɓe na 2023 a Najeriya.

Shugabancin jam'iyyar APC na ƙasa mai mulki a Najeriya ya dakatar da babban taron jam'iyyar a Jihar Oyo saboda zargin yunƙurin maguɗin zaɓe.

Shugaban APC na riƙo, Gwamna Mai Mala Buni, shi ne ya sanar da matakin cikin wata sanarwa da sakataren jam'iyyar, John James Akpanudoedehe, ya fitar a safiyar Asabar.

Ya ce dakatarwar ta zama dole domin aiwatar da zaɓen shugabannin jam'iyyar cikin gaskiya a Oyo. Ana zargin wasu 'ya'yan jam'iyyar da buga takardun zaɓe na bogi, in ji sanarwar.

"Shugaban jam'iyya na ƙasa ya umarci kwamatin shirya taron a Oyo da su koma sakatariyar jam'iyyar domin tattaunawa," a cewar sanarwar.

Jam'iyyar APC na gudanar da taruka a faɗin Najeriya da zummar zaɓen shugabanninta a kowane mataki yau Asabar.