2023: Mulkin Nijeriya Ba Na Wasu Gungun Mutane Ba Ne Su Kadai---Tambuwal

2023: Mulkin Nijeriya Ba Na Wasu Gungun Mutane Ba Ne Su Kadai---Tambuwal

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya tabbatar da cewa ba wasu gungun mutane a cikin kowane addini ko kabila da za su  mayar da mulkin Nijeriya na su ne su kadai, ban da wasu mutane a kasar nan.

Gwaman Tambuwal ya yi wannan hasashen ne a lokacin da shugaban kungiyar Kiristocin Nijeriya Rev, Ayokunle Samson Olasupo  ya kai masa ziyarar ban girma a fadar gwamnatin jiha a birnin Sakkwato.

A cewar Gwamna Tambuwal shugabancin Nijeriya lamari ne da kowane dan Nijeriya zai iya yin sa, ba wani da ke iya korar wani daga cikin kasar abu ne da ake tare domin cigaban kasa baki daya.

<

p style="text-align: justify;">Nijeriya na bukatar shugaba da yake da fahimtar lamurra duk yanda suka shige duhu ya rika tafiyar da mulki ba tare da sanya bambancin addini ko kabila ba.

Ya ce da ana bin karantarwar addini yanda yakamata ba abin da zai sa a rika fada da juna.

Ya jinjinawa Sarkin Musulmi da shugaban kiristocin kan kokarinsu na samar da zaman lafiya da hadin kai, hakan ke nuna Sakkwato gida ce ga kowane dan Nijeriya ba tare da la’akari da bmbancin addini addininka ko kabilarka ba.