Abin Da Ya Sa Zaben Tambuwal, Wamakko Da Gwanda Bai Kammala Ba---INEC
Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da Gwanda Gobir da sauran ‘yan takara 10 da suka nemi kujeru a majalisar wakilai ta tarayyar Nijeriya zabensu bai kammala ba kaamar yada hukumar zabe ta kasa reshen jihar Sakkwato ta sanar a cibiyoyin tattara sakamakon zabe daban-daban dake cikin jiha.
Gwamnan Sakkwato da yake neman kujerar Sanata a yankin kudancin Sakkwato cikin jam'iyar PDP shi ke kan gaba kafin a aiyana zabensa matsayin wanda bai kammala ba.
Farfesa Shehu Usman Gobir a sakamakon zaben da ya fitar Tambuwal na kan gaban Sanata Ibrahim Danbaba Dambuwa da kuri’a dubu 7,859 in da mutum 83,036 ba su yi zabe ba don haka za a ba su dama su yi zabe.
Sanata Aliyu Wamakko da yake neman sake komawa Sanata da zai wakilci yankin Sakkwato ta Arewa a jam’iyar APC shi ma zabensa bai kammala ba.
Farfesa Ibrahim Magawata a sakamakon da ya bayyana Sanata Wamakko na gaban Mataimakin Gwamnan Sakkwato Honarabul Manir Dan’iya da kuri’a dubu 11,732, mutum dubu 121, 010 ne ba su yi zabe ba don haka za a ba su dama kafin a aiyana wanda ya yi nasara.
Honarabul Shu’aibu Gwanda Gobir ne gaban Honarabul Ibrahim Lamido dake neman kujerar Sakkwato ta gabas jami'in tattara zabe ya aiyana zaben su bai kammala ba.
Farfesa Abubakar Abdullahi Bagudo a lokacin da ya kammala tattara sakamakon zaben gabascin Sakkwato ya sanar da cewa jam'iyar PDP ce kan gaba a zaben Sanata da kuri'a 2551, yawan kuri'un da ba a yi zabe ba sun kai dubu 67, 602, a tsarin doka zaben bai kammala ba sai an yi wa wadan nan mutanen zabe.
A cikin kujerar 'yan majalisar wakillai guda 11, daya ce kawai wadda ake wakiltar kananan hukumomin Yabo da Shagari ta kammala in da jam'iyar PDP ta samu nasara aka kayar da wanda ke sama na jam'iyar APC.
managarciya