Shugabanni A Matakin Jiha: APC Sakkwato Ta Aminta Da Zaɓen Sulhu  Babu Hamayya

Shugaban jam'iyar na riƙo a  matakin jiha Alhaji Isah Sadik Achida ya sanarwa mahalarta taron shirin da aka gudanar domin samun nasarar jam'iyar a zaɓen da za a gudanar.

Shugabanni A Matakin Jiha: APC Sakkwato Ta Aminta Da Zaɓen Sulhu  Babu Hamayya
Tutar APC

Shugabanni A Matakin Jiha: APC Sakkwato Ta Aminta Da Zaɓen Sulhu  Babu Hamayya

Taron masu ruwa da tsaki da jam'iyar APC ta gudanar a ofishinta domin tunkarar zaɓen shugabannin jam'iya matakin jihar Sakkwato, sun aminta da zaɓen ya kasance silhu waton babu hamayya.
Shugaban jam'iyar na riƙo a  matakin jiha Alhaji Isah Sadik Achida ya sanarwa mahalarta taron shirin da aka gudanar domin samun nasarar jam'iyar a zaɓen da za a gudanar.
Ya bayyana cewa zaɓen za su tsaya ne kan dokar da jam'iya ta tanadar .
Mahalarta taron sun aminta da yin zaɓen cikin sulhu ba hamayya domin ƙara samun haɗin kai a tsakanin mambobin jam'iyya.
Shugaban gudanar da zaɓen da uwar jam'iyya ta turo Alhaji Sulaiman Usman  iyan Akko, ya yi kira ga mambobin APC su zama masu bin doka da oda a lokacin gudanar da zaɓen.