Daga Habu Rabeel, Gombe
Ɗan takaran Gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Gombe, Alhaji Muhammad Jibrin Dan Barde, ya yi wata gana ta musamman da mambobin ƙungiyar wadanda suka yi takaran kujerun majalisun jihar Gombe na jam'iyyar PDP da suka sayi form suka shiga zaben fidda gwani.
Da yake karbar mambobin kungiyar Muhammad Jibrin Dan Barde, ya godewa mambobin ƙungiyar saboda jajircewan su da kuma nuna kauna wa jam'iyyar su ta PDP har suke kokarin taya shi yakin neman zabe dan kwace mulki a hannun APC.
Dan Barde, yace yana mai tabbatar musu da cewa babu wanda ya faɗi a zabe a cikin su matuƙar dai suka tsaya sukayi aiki tuƙuru don samun nasarar PDP wanda dukkan alamu sun bayyana a fili rashin iya mulkin APC yasa kowa ya gaji da ita.
Sannan yace kowa a jihar Gombe yasan cewa komai ya tabarbare musamman harkar kiwon lafiya da Ilimi da noma da samar da ayyukan yi ga matasa da sauran fannoni na rayuwa daban daban shi idan yazo zai yi abunda ya kamata dan farfado da su.
Daga nan sai ya yi musu albishir da cewa shi gwamnatin da zai kafa gwamnati ce ta mutane ba nasa shi kaɗai ba saboda duk abunda zai yi sai ya nemi shawarin al'umma kafin ya aiwatar.
Da yake nasa jawabi Shugaban ƙungiyar na jihar Gombe, wato Gombe state PDP House of Assembly Aspirants Forum, Alhaji Sadeeq Gidado, Bargan Gombe, ya shaidawa dan takarar cewa su kaɗai sun isa su tallafa masa har zuwa lokacin babban zabe.
Alhaji Sadeeq Gidado, yace sun shirya makaman yakin su tsaf domin taya shi tunkarar abokin takarar sa a zaben dake tafe na shekarar 2023.
Ya kara da cewa idan akwai wani aikin da Muhammad Jibrin Dan Barde yake son ƙungiyar ta yi masa to ya faɗa musu za su haɗa kai su yi gaba ɗaya domin yakin ba nasa shi kadai bane nasu ne domin su ne za su wuce masa gaba.
A jawaban su mabanbanta jagororin yankin Gombe ta arewa da Gombe ta tsakiya da Gombe ta kudu Honourabul El-k
ana da Honurabul Umar Adamu Pindiga da Honurabul Musa Kallamu, cewa suka yi sun tsaya ne a madadin yankunan su kuma kansu a hade yake za su kawo kuri'un yankin a dungule.