Ana Tunkarar  2023, Masu Ruwa da Tsakin PDP a Sokoto Sun Koma APC

Ana Tunkarar  2023, Masu Ruwa da Tsakin PDP a Sokoto Sun Koma APC

Wasu jiga-jigai kuma masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDP sun bayyana sauya sheka a jihar Sokoto zuwa jam'iyya mai ci ta APC, Managarciya  ta ruwaito. 

 Jam'iyyun APC da PDP na ci gaba da fuskantar kaura a 'yan kwanakin nan yayin da ake tunkarar zaben 2023. 
A cewar wata sanarwa da Bashar Abubakar, hadimin Sanata Aliyu Wammako ya fitar a ranar Talata 1 ga watan Nuwamba, wannan  ya faru ne a karamar hukumar Isa dake jihar. 
Bashar ya kuma bayyana cewa, wadanda suka sauya shekan zuwa APC sun kasance shugabanni kuma masu ruwa da tsaki a yankunan Turba, Bafarawa da Bargaja da dai wasu fitattun yankunan jihar. 
A cewarsa, wadanda suka sauyan shekan sun samu tarba daga dan takarar sanatan mazabar, Alhaji Ibrahim Lamido a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar. Bashar ya nakalto Lamido na ba sabbin mambobin jam'iyyar tabbacin samun wuri a APC, kuma za a dauke su kamar tsoffin mambobinta a ko'ina a kasar nan.
Dan takarar sanatanm wanda Alhaji Kabiru Sarkin-Fulani ya wakilta, shugaban APC na karamar hukumar Goronyo ya yi maraba  matuka da zuwa cikin  jam'iyyar. 
Ya kuma yaba da irin jajircewar da suka yi na daukar wannan mataki, sannan ya kalubalance su da su kara kokari wajen ciyar da APC da ma jihar baki daga gaba.
Da suke bayyana dalilin barin PDP, wadanda suka sauya shekan sun ce sam sun rasa kwarin gwiwar hango nasara a PDP a zabe mai zuwa.