Shugaba Buhari Zai Naɗa Wani Sabon Minista A Nijeriya
Shugaba Buhari Zai Naɗa Wani Sabon Minista A Nijeriya
Daga : Janaidu Amadu Doro.
Shugaban ƙasa Muhammdu Buhari ya miƙa sunan Mu’azu Jaji Sambo daga jihar Taraba a gaban majalisar dattijai domin naɗashi a matsayin sabon minista.
Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke karanto wata takarda da shugaban ya rubutawa zauren a yau Talata.
Shugaba Buhari ya buƙaci majalisar dattawa da ta tantance tare da tabbatar da Ma’azu Jaji domin naɗa shi a matsayin sabon minista.
Tsawon lokaci bayan da Buhari ya saukar da ministocinsa guda biyu sai a yanzu ya aika sunan ɗaya daga jihar Taraba daga Kano ba a tura kowa ba har yanzu.
managarciya