Kudirinmu Manoman Masara Su Dogara Da Kansu Ba Tare Da Bashi Ba-----Bello Annur

"Shekaru hudu da mu ka yi mun samu wayewa  yadda za mu bi mu dogara da kanmu ba sai Gwamnati ta ba mu bashi ba.dan bashi da muke amsa a baya ya taimaka wajan dogara da kanmu. Kuma mun tsayu da kafafuwan mu. in ji Shugaban. Dan haka a wannan zango na biyu da muka shiga na mulkin mu, za mu hada gwiwa da Gwamnati da Kamfanoni,dan sarafa amfanin gona da zai taimaki Manoman mu wajan bunkasa Noman da kuma cin gajiyar sa a saukake.

Kudirinmu Manoman Masara Su Dogara Da Kansu Ba Tare Da Bashi Ba-----Bello Annur
 

Daga Hussaini Yero

 

Shugaban Kungiyar Manoman na Kasa ,Bello Abubakar Annur Jagaban Azara ,ya bayyana kudirin sa na ganin Manoman Masara sun dogara da kansu ba tare da bashi ba daga Gwamnati ko kamfani ba.

 

 Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke tattaunawa da manaima labarai a ofishinsa da ke Abuja.

 
Jagaban Azara ya kara da cewa, Manoman Masara na daya daga cikin wadanda ke taka rawa wajan ganin ansamar da isashe abinci a Kasar nan da ma wajanta.kuma Masara na daya daga cikin amafanin gona da ke habaka arzikin wannan kasar ta mu.in ji Shugaban.
 
"Shekaru hudu da mu ka yi mun samu wayewa  yadda za mu bi mu dogara da kanmu ba sai Gwamnati ta ba mu bashi ba.dan bashi da muke amsa a baya ya taimaka wajan dogara da kanmu. Kuma mun tsayu da kafafuwan mu. in ji Shugaban.
 
Dan haka a wannan zango na biyu da muka shiga na mulkin mu, za mu hada gwiwa da Gwamnati da Kamfanoni,dan sarafa amfanin gona da zai taimaki Manoman mu wajan bunkasa Noman da kuma cin gajiyar sa a saukake.
 
"Da ya koma kan batun ayyukan Kungiyar da nasarorin da ta samu a loakacin zango sa na farko, Shugaban ya bayyana cewa, kungiyoyin na da manbobi dubu dari da ashirin. Amma yanzu kuwa muna manbobi sama da Manoma miliyan biyar a fadin Kasar nan.wannan Babbar na sara ce a garemu.sai Kuma yanzu haka wannan Kungiyar ta mallaki gidaje guda shida a cikin Abuja a Jabi kowane gida bene ne hawa biyu akillace da kuma tarakata mai girbe amfani gona ta zamani .muna alfahari da wannna nasara da Allah ya bamu Kuma ina mai tabbatar maka da cewa babu wata kungiya irin tamu da ta mallaki kadara irin tamu. muna godiya akan haka.