'Yan Kasuwa Da Direbobi Na Cigaba Da Kin Karbar Tsoffin Kudi Duk Da Umarnin Kotun Koli 

'Yan Kasuwa Da Direbobi Na Cigaba Da Kin Karbar Tsoffin Kudi Duk Da Umarnin Kotun Koli 

 

Duk da umarnin kotun koli kan tsoffin kudi, Daily Sun ta binciko yadda masu sana'o'i da kuma direbobi a kwaryar birnin Legas ke cigaba da kin karbar tsoffin kudin tare da bayyana cewa sai sun ji amincewar Shugaba Muhammadu Buhari kan hukuncin kotun. 

Tun da farko kotun kolin ta yi umarnin cewa a cigaba da karbar tsohon kudi har zuwa 31 ga watan Disambar 2023, inda ta yi watsi da wa'adin babban bankin kasa CBN. 
Sai dai, a sabon hukuncin da kotun kolin ta yanke ranar Juma'a, kotun kolin ta ce tsohon kudin zai cigaba da zama halattace har zuwa 31 ga watan Disambar 2023, tare da yin watsi da sauya fasalin takardun kudin. 
Kotun kuma ta ce ba a bai wa mutane isasshen wa'adi ba idan akayi la'akari da sashe na 20 na kudin dokar CBN na 2007. 
Bisa wannan dalili, babban bankin kasa zai tsawaita halaccin kudin zuwa 31 ga watan Disamba, 2023, bisa dalilin cewa kasashe da dama suna barin sabo da tsohon kudi su zagaya a tare akalla na shekara guda. 
Idan za a iya tunawa a Disambar 2022, babban bankin kasa CBN ya sanar da sauya fasalin N200, N500 da kuma 1,000 daga 10 ga watan Fabrairu 2023. 
Dalilin haka, gwamnonin kasar 16 suka nuna rashin amincewa da dokar, tare da shigar da karar gwamnatin tarayya, su na rokon kotun da ta dakatar da dokar.