Tsohon Minista Ya Tona Ainihin Wadanda Su ke Hana a Gyara Wutar Lantarkin Najeriya

Tsohon Minista Ya Tona Ainihin Wadanda Su ke Hana a Gyara Wutar Lantarkin Najeriya

Barth Nnaji wanda ya yi Ministan harkokin wutar lantarki a kasar nan, ya yi bayani game da abin da ya ke kawo cikas har kullum. A wata zantawa da aka yi da shi a gidan rediyon Flo FM da ke garin Umuahia a jihar Abia, Farfesa Barth Nnaji ya haska matsalar Najeriya. 
Farfesan ya zargi manyan dillalan janareto da masu shigo da man dizil da kawo matsala wajen kokarin ganin an samar da isasshen wuta. 
Barth Nnaji yake cewa daukewar da babbar tashar Najeriya ta ke yi matsala ce da aka gagaro kawo karshenta, kuma abin damuwa ne. 
Yanzu haka Nnaji shi ne shugaban kamfanin Geometric Power da ke garin Aba, ya ce masu janaerto da harkar dizil sun zama ala-ka-kai. 
"Akwai bangarori biyu idan ana maganar masu hana ruwa gudu a bangaren nan – masu shigo da man dizil da kuma masu injinan janero. 
Najeriya na cikin manyan inda ake amfani da janaretoci saboda matukar bukatar wutanmu, ‘yan kasuwa ba za su so daukewar wuta ba. Masu shigo da dizil su na ganin cewa idan lantarki ya zauna, kasuwancinsu zai lalace."