SHAHIDAH: Labarin Kan  Ƙaddarar Rayuwar Da Ta Afkawa Wata Matashiya

SHAHIDAH: Labarin Kan  Ƙaddarar Rayuwar Da Ta Afkawa Wata Matashiya

SHAHIDAH: Labarin Kan  Ƙaddarar Rayuwa

Na: Rukayya Ibrahim Lawal (Ummu Inteesar)


AREWA WRITERS ASSOCIATION
(Arewa ginshikin al'umma)

Tsokaci.

Ƙaddara ce ta sarƙafe ni ta min ɗaurin talala izuwa ga rayuwa da abin da ya sha bamban da abin da na ke muradi, kuma cikar burina.
Na zaɓi na yi yaƙi da kowa koda hakan yana nufin rayuka za su salwanta.
Sai dai abin ya zo mun da bazata, bayan da na shiga ayarin masu fafutukar su ci gaba da numfashi a doron ƙasa.

GAJEREN LABARI: 1 TO END

Cikin yanayin firgici da rikicewar ƙwaƙwalwa nake bin gawar mijina da kallo.
Kunnuwana sun kasa gasgata abin da suka jiyo min _'wai Usman ya rasu.'_
Matsowa na yi daf da shimfiɗar na durƙusa tare da fashewa da kuka, tuni hawayen nadama suka fara ambaliya a fuskata.

Tun ranar farko dana fara ɗora idona akansa ban taɓa jin sonsa ko digon tausayinsa ba a zuciyata sai yau da ya zama gawa.

"Ga Usman nan, shi ne zaɓin da muka yi miki a matsayinmu na mahaifanki kuma ba makawa sai kin aure shi." Kalaman Abbana suka dinga dawo min a massarafar jina tamkar yanzu yake furta su.

Sai kuma na tuna amsar dana ba shi.
"Abba ka min rai wallahi ni Salim nake so, da shi na tsara rayuwata matuƙar kuka raba ni da shi to komai ya faru ku ne sila."

Kafin na yi nisa a tafkin tunani na ji muryar yayan Usman yana faɗar "Ku fito da gawar." Sannan ya mayar da akalar zancensa a kaina "Shi kenan hankalinki ya kwanta ko Shahidah? Kin kashe Usman ga duniyar nan ya bar miki, ki zauna ki yi gadinta. In dai duniya ce wanda bai zo ba ma tana jiransa." Yana gama faɗa ya yi fuu ya bi bayan waɗanda suka ɗauki gawar a hasale.
Nan da nan wutar ƙuncin da ke zuciyata ta ci gaba da ruruwa, sautin kukana ya daɗu.
Haƙiƙa ina cikin matsanancin tashin hankali mara misali. Jinjirar dake hannuna na ƙara ƙanƙamewa a jikina ina mai ci gaba da kukan da ba mai rarrashi.
 Domin kowa haushina yake ji ba wanda ya zo kusa da ni da sunan jajanta min mutuwar mijina, sai dai masu jifana da munanan kalamai. Sakamakon shuɗaɗɗen laifin dana aikata a watannin baya.

Da dare ina kwance kan gadona cikin matsananciyar damuwa, zafin ya haɗe min biyu ga ciwon zuci ga na gangar jiki. Abin da ya fi damu na a yanzu shi ne matsalar da Usman ya mutu ya bar mu a ciki. Ƙara rungume 'yata na yi, ina jin sonta na yawo a jinina. Sai dai na sani ko da yaushe mutuwa za ta iya mana yankan ƙauna kamar yadda ta ɗauke Usman a yau.

Share hawayena na yi "Ka cutar da ni Usman ga shi ka tafi ka bar ni da tabon raunin da ka min, ga 'yarka mai ɗauke da cutar ƙanjamau. Yanzu wa zai kula da wannan talikar bayan raina? Zuwa yanzu ko ƴaƴan jaba sun fi mu farinjini a idon jama'a. Ko da yake iyayena ne silar komai da ya same ni a yau."

Ina zuwa nan tunani ya ɗebe ni ya maida ni shekaru uku baya, yayin da majigin ƙwaƙwalwata ya fara hasko min abubuwan da suka faru a wancan lokacin.

Ni da Salim mun kasance muna matuƙar ƙaunar junanmu, mun riga mun gama tsara irin rayuwar da zamu yi a gidan aurenmu.

Kwatsam sai iyayena suka saka gatari suka datse mana wannan kyakkyawan fatan namu, tare da toshe duk wata hanyar farincikinmu ta silar Usman da ya shigo rayuwata daga sama.
A lokacin ne tseren ya fara yayin da na yi barazanar cewa muddin aka raba ni da farincikina to komai ya faru su ne sila.

Iyayena suka yi kunnen uwar shegu da wannan zancen nawa, a ganin su duk barazana ce. Da an ɗaura auren zan haƙura na rungumi ƙaddara.
 Wannan dalilin ya saka abbana ya saka aka kira masa Salim ya ba shi haƙuri tare da yi masa umurnin nisanta daga gare ni.

"Ka yi hakuri Salim ƙaddara ta riga fata, dama can an rubuta Shahidah ba matarka ba ce..."
Kalaman da suka daki dodon kunnena kenan yayin da nake ƙoƙarin fitowa daga gidanmu.

Idona ya faɗa cikin na Salim dake fitar da ƙwallar baƙinciki, bai iya cewa komai ba, ya juya ya bar abbanmu nan tsaye.

"Abba kada ka katse mana zaren farincikinmu da walwalarmu, ina jaddada maka komai zai iya faruwa idan na rasa Salim shi ne farincikina."
Na furta muryata na rawa. 
"Ai kuwa sai dai ki tabbata a cikin ƙunci domin bakin alƙalami ya riga ya bushe nan da kwana bakwai za a ɗaura aurenki da Usman." 
Abbana ya furta cikin rashin kula.

Da gudu na juya zuwa cikin gidan ina rushewa da matsanancin kuka.
Ana cewa idan hankali ya ɓata hankali ake sakawa ya nemo shi. Hakan ce ta faru, amma ni yayin da na aika hankalin don nemo nawa sai suka ɓata gabaɗaya. Domin kuwa zuciyata ce ta bushe, idanunta suka makance. 
Na sha alwashin cewa sai na ƙuntata rayuwar Usman da ya zama silar lalata farincikina.

Haka na rayu tsawon sati ɗaya a cikin makantacciyar duniya, duniyar da ba komai a cikinta sai duhun ƙunci da damuwa. Duniyar da take cike da mutane masu son kai.
Ranar wata Asabar aka ɗaura aurena da Usman, wadda wannan ranar ta kasance cikin baƙin kundi na tarihin rayuwata.

Rayuwar gidan aure rayuwa ce da kowanne mahaluƙi ke saka rai da samun farinciki da nutsuwa. Sai dai a gurin Usman akasin hakan ce ta kasance. Domin kuwa kodayaushe ba ni da aiki sai ƙuntata masa.

Sai da na tabbatar na saka almakashi na faffarka duk wani farincikin Usman sa'annan na samu 'yar nutsuwa. Na hana masa duk wani haƙƙinsa da ya rataya a wuyana, saboda ƙiyayya da jin haushin raba ni da masoyina da ya yi.

 Yayin da Salim ya kasance maƙale a can ƙasan zuciyata. Kuma ban daina tunanin mallakarsa ba a rayuwa na yi imani cewa _'inda rai da rabo'_ watarana zan mallake shi.

Wannan abin ya jefa mijina a cikin mawuyacin hali tun yana haƙuri da munanan ɗabi'una har ya gagara riƙe kansa ya fara neman matan banza a waje. Wanda duk nice silar hakan. 
Sai da muka shafe shekara ɗaya da rabi a hakan kafin na fara yarda da shi a matsayin mijin ƙaddarata.

Ban sani ba ashe hakan ya bar _'baya da ƙura.'_ ashe masifa na buɗewa ƙofa ta shigo gidan aurena.
A cikin shekara ta biyu da aurenmu ciki ya bayyana a jikina. wannan cikin ya ƙara ƙuntata duniyata domin har yanzu tsakanina da mijina 'bata canza zani ba.' 

Watarana na ji canjin yanayi a jikina hakan yasa na dangana da asibiti.
Sai da aka min test kala-kala kafin a iya gano matsalar da take addabar rayuwata.

"Hmm! To da farko dai ina son in miki tuni da cewa yin imani da ƙaddara kyakkyawa ko akasin haka yana ɗaya daga cikin shika-shikan imani..."
Tun kan likitan ya ƙarasa zancensa nake jin gabana na lugude zuciyata na ba ni siginal ɗin cewa zai min mummunan albishir ne.

"Meke damuna likita?"
Na tambaya a dabarbarce.
"Kina ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato H.I.V(cutar ƙanjamau) amma...."

Ban jira na ji ƙarshen zancen ba na zabura na miƙe tamkar hauka sabon kamu.
"Innalillahi wa Inna ilahir rajiun! Ka cuce ni Usman, da ma kai ɗan Akuya ne ban sani ba?"

Hawaye jaɓe-jaɓe a fuskata na fice daga ofishin likitan ba tare da na karɓi takardar gwajin ba.
Ina isa gida na fara zazzaga masifa, tun daga tsakar gida
"Ina ɗan akuyan yake?" Da wannan kalmar na shiga ɗakina a maimakon sallama. Inda na tarad da shi zaune.

"Waye ɗan akuyan wai?"

"Da wani ne a ɗakin bayan mu biyu?" Na mayar masa da tambaya. Sannan na ci gaba da cewa "Ina zamana ƙalau a cikin farinciki tare da mai ƙaunata da gaskiya ka zo ka farraƙa mu, ashe akwai abin da maƙetaciyar zuciyarka ta ƙitsa maka. Kana sane da ƙamaya-mayar da ka ɗebo, shi ne ka shafa min."

A fusace ya miƙe tsaye "Ni fa ban fuskanci inda kika dosa ba, ki fito min a mutum kawai malama."

"Dawowata kenan daga ganin likita, kuma ya tabbatar min da cewa ina ɗauke da cutar ƙanjamau, kuma sarai ka san cewa ni ba fasiƙa ba ce kenan _'Ta tabbata satar Hajiya a makka."_

Jin wannan zancen ya bayyanar da damuwa ƙarara a fuskarsa, jikinsa ya yi sanyi tamkar kazar da aka jefa da gishiri.
Da wannan damar na yi amfani na shiga rigar mutuncinsa na yi kaca-kaca da ita.

A sukwane ya ƙaraso inda nake tare da falle ni da lafiyayyun mari har guda biyu.

"Me ya saka ne ke baki san zuru ba? Ai duk abin da ya samu shamuwa watan bakwai ne ya ja mata. Da kin sauke min haƙƙoƙina da suke kanki da duk haka bata faru ba. Amma da yake kin biye wa huɗubar wahalallen tunaninki, yau ga abin da kika janyo mana." Ya sauke zancen yana huci tamkar kumurci.

 Sannan ya ƙulla igiyar zancen da fadar 
"Ni ba fasiƙi ba ne, Allah ne shaidata. Inda wanda za a tuhuma a kan lalacewata to ke ce..." Tamkar rediyo haka ya ci gaba da zazzaga min kwandon rashin arziƙi.

Ni dai ba baki sai kunne don kuwa ƙamewa na yi, na zuba masa na mujiya.
Ashe da gaske ne da ake cewa  _mai haƙuri bai iya fishi ba?_

Tun da na ke da Usman kimanin shekaru biyu kenan, amma bai taɓa ɗaga mini murya irin na ranar ba, duk kuwa da irin cin kashin da nake yi masa.
A haka ya ƙaraci masifarsa ya fice daga gidan cikin damuwa.

Duk wannan abin bai saka na sauko daga dokin naƙi da nake sukuwa a kai ba.
"Kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha, da ni kake zancen sai na ɗauki fansar marina da ka yi, banza kawai."
Na furta cikin ɗaga murya.

Kwanci tashi asarar mai rai a haka aka shafe watanni biyu, lokacin da ya zo dai dai da watan haihuwata.

Watarana da misalin ƙarfe 1 na dare, Usman ya fara bacci kenan na sulale tamkar macijiya na fice zuwa kitchen.
Bakomai na je nema ba, face abin da zai zama silar rabuwata da Usman rabuwa ta har abada.
Ban sani ba ashe ƙarar yamutsa kwanukan da nake ya farkad da shi.
Ko da na dawo ɗakin na tarar da shi a kwance ya buɗe idonsa.

"Me kika fita yi yanzu cikin daren nan?" Ban ce masa kanzil ba, sai matsowa da nake yi hannuwana suna baya.

Kafin ya sami damar yin wata magana na shammace shi na caka masa cokali mai yatsun dake hannuna a ciki da iya ƙarfina.

"Ah! Inalillahi wa Inna ilaihir raji'un! Heedah kashe ni kike son yi?"
Ya furta da ƙyar. Da ganin yadda ya dafe cikinsa ka san yana jin jiki.
Ba kunya na kalli cikin ƙwayar idonsa na ce
 "Tabbas ka canka dai dai wannan shi ne abin da zai faru da kai matuƙar baka sawwaƙe mini ba. Ka yi sa'a ma da ban sami nasarar ganin wuƙa ba, da ita zan daɓa maka. Na tsane ka Usman, na tsane ka."
Ina kallon shi yana yunƙurin kiran waya, ban jira na ji wa zai kira ba na ja mayafina na fice daga gidan  zuwa titi.
Da ƙyar na sami adaidaita sahu na hau zuwa gidanmu, bayan na riga na gama ƙitsa abin da zan wanke kaina daga tuhuma.

Washegarin ranar labarin abin da na aikata ya riski abbana. Bai bi ta kaina ba shi da umma suka nufi asibiti don duba lafiyar Usman.
Bayan dawowar su suka shiga tuhumata ƙarin bayani a kan abin da ya faru jiya.
Kukan munafurci na fashe da shi Sannan na shiga shirga musu ƙarya. Da abin da aka yi da wanda ba a yi ba duk na faɗa na ce an yi.
Bayan na gama ɗaure shi da igiyar zargi na ɗora da cewa
"Abba Usman ba ɗan goyo ba ne, duk irin ƙaunar da kuka nuna masa ashe shirin yaudararku yake yi  _'fasiƙi ne na ƙarshe'_  haƙuri kawai nake da shi, gashi garin yawon fasiƙancinsa ya ɗebo mana cuta mai karya garkuwar jiki. Jiya ma da wata ya shigo min gida, da na yi magana shi ne ya hau ni da zagi da duka. A yunƙurina na kare kaina na shi ne soka masa cokali mai yatsu a ciki."

Ina zuwa nan na fashe da kukan munafurci. Ran iyayena ya kai ƙoluluwar ɓaci. Fuskantar hakan da na yi ya saka na dage a ci gaba da rera kukana.
Wannan dalilin ne ya saka abba ya bar ni na zauna a gida, kuma ya ɗauki zafi da Usman sosai ba tare da bincike ba. Haka bai kuma waiwayar lafiyar Usman ba.
Bayan Usman ya warke sarai ya nufo gidanmu da nufin biko. Bayan ya saurari duk irin ƙorafin iyayena a kansa a nan ya warware musu zare da abawa. 
Sannan ya ɗora da cewa

 "Ba don komai na yafe mata haƙƙina ba, sai don albarkacin wannan cikin da ke jikinta, da kuma cutar dake tattare da ita. A yanzu ko Salim da take mutuwar so na tabbatar ba zai iya zama da ita ba, gara ta koma mu rufawa juna asiri."

Sosai Abba ya gamsu da waɗannan jawaban na shi. Cikin fishi ya dube ni "To mutuniyar banza ki sani kina haihuwa kika gama jego zaki koma ɗakinki."

Nan ya ƙara ba wa Usman haƙuri akan abubuwan da suka faru ya sallame shi ya tafi.
Bayan shuɗewar kwana biyu na haifi 'yata mace kyakkyawa. Yarinyar ta shiga zuciyata sosai ta yadda ban yi tsammani ba.
Bayan kwana biyu da haihuwar ta ta fara ciwon da ba mu gane masa ba, hakan ya sa muka je asibiti.
Bayan yin dogon bincike likitoci suka gano cewar yarinyar an haife ta ne ɗauke da cutar ƙanjamau.
Lamarin da ya gigita duniyata tare da saka ni a ruɗa ni.
" Jinjira ɗauke da wannan cutar to garin yaya?" umma ta tambaya.

Likita ya mana cikakken bayani a kan cewa za a iya haihuwar yaro da cutar matuƙar iyayensa na ɗauke da ita, kuma mahaifiyar ba ta kiyaye ƙa'idar shan magani yadda ya kamata sai ta zame masa gado.
Bayan watanni biyu na koma gidan mijina. Yayin da yake ci gaba da haƙuri da ni.
Haka zarukan tunanina suka ci gaba da ƙulluwa har zuwa ranar yau da safe. Ya shirya za shi aiki ya ce da ni
"Heedah ga amanar 'yata nan, ki kula da ita sosai ko bayan raina ina roƙon wannan alfarmar. Ina ji a jikina tamkar mutuwa na kusanto ni."
"To ka mutu mana, zan yi farinciki da hakan domin ko ba komai na san zan koma ga masoyina."
Girgiza kai kawai ya yi ya ce "Ni na tafi."
Da harara na raka shi tare da faɗar 'Allah ya raka taki gona.'
Daga wannan fitar ne bai dawo ba, sai gawarsa aka kawo mini wai ya yi hatsari da mota.

"Ina take matsiyaciyar? Ai sai ki fito zaman gidan nan ya ƙare miki. Kuma ki jira yi sammaci don kuwa ruhin ɗan'uwana ba zai tafi a banza ba."
Wannan zancen da na jiyo daga ƙofa ne ya yi nasarar tsinke zaren tunanina. Zabura na yi da sauri kamar an tsikare ni.
Ina zuwa na ga yaya Amina (Babbar yayar Usman, wacce ya taso a hannunta.)
Hannu ta saka ta ɗauke ni da lafiyayyen mari tare da  wurga mini wata uwar uwar harara sa'annan ta ture ni gefe, tare da yi wa ƙannenta mata umurni, suka shiga ɗakina suka fara watso min kayana waje.
Hakan nan suka miƙo min 'yata suka rufe ɗakin.
"To ai sai ki tashi ki tattare 'yan komatsanki ki bar gidan tun da ba da kuɗin tsohonki aka gina ba."
Yaya Amina ce ke wannan zancen yayin da Maryam ta karɓe da.
"Ina tunanin iya wannan ne mallakinki domin sanin kanki ne ba a kawo ki da komai ba a gidan nan. Wannan kayan ma albarkacin Amatullah ne zamu bar miki. Ko ba komai dai ita jininmu ce."

"Illar matsiyaci kenan, ka janyo shi inuwa ya yi ƙoƙarin tura ka rana."

Cewar Aisha da ke tsaye a kaina.
Ni dai ban ce musu uffan ba, kukana kawai nake. Cike da raɗaɗin zuciya na haɗa 'yan tarkacen nawa na goya 'yata na bar musu gidan.
Da isata gida na labartawa iyayena abin da ya faru. Haka nan kuma na kwashe duk abin da ya faru a rayuwar aurena da Usman na faɗa musu.

Abba cikin tsananin damuwa ya kalle ni
"Ki gafarta mini 'yar nan, tabbas tun farko da ma kin faɗa, idan muka yi haɗin nan duk abin da ya faru mu ne sila. Kaicona da na biye wa son abin duniya!. Dama bahaushe ya ce  _'duk wanda ya hau motar kwaɗayi ba inda za ta sauke shi sai tashar wulaƙanci.'_
Nisawa ya yi sannan ya ce
"Kwanan nan nake samun labarin Salim ya sami taɓin ƙwaƙwalwa dalilin rayuwar shaye-shaye da ya faɗa bayan rasa ki. Haƙiƙa na ji matuƙar ba daɗi, sai yau na ƙara tabbatar da cewa na shiga haƙƙinku dana raba soyayyarku. Don Allah ki yafe min 'yata."
Ko da na sami labarin matsalar da Salim ya faɗa ciki sai zuciyata ta buga da ƙarfi. Ban farka ba sai a gadon asibiti.
Farkawad da na yi fatan ace na mutu da yinta, domin abin da kunnena ya jiye min, gara ma ace na mutu a zahiri. Domin a yanzu ma a mace nake a baɗini.
Wai _'Amatullah ta mutu.'_ na jima ina mirza kalmar a maniƙar niƙa kalamaina amma ta gagara yin laushi, ta yadda zan fuskance ta.
"Shi kenan abba haƙiƙa kun cutar da rayuwata, Salim ya haɗu da taɓin ƙwaƙwalwa ta silata, 'yar da ta rage min farinciki ta mutu. Ni ma rayuwata bata da tabbas. Haƙiƙa duk abin da ya faru kune sila."
Na furta da raunanniyar murya, hawaye na bin kuncina.


Ƙarshe.