Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 10 Sun Yi Garkuwa da 45 a Sakkwato
‘Yan bindiga da yake da yawan gaske sun shiga kauyukka uku a karamar hukumar Illela a jihar Sakkwato in da suka kashe muta ne 10, suka yi garkuwa da 45 suka sace shanu 200 a cikin kwana biyu.
Majiyar ta ce Maharan sun shiga kauyen Karambi a shekaran jiya ba su taba kowa ba amma sun tafi gargen shanu da mutane ke a jewa kafin tafiya da su a kasauwar Illela a nan suka sace shanuwa 200, daga nan suka wuce Damba a yankin Gigane suka yi garkuwa da mutum 45 mata da maza da kananan yara.
“A jiya(Talata) bayan sallar magariba sun ka shigo garinmu Buwadai mutanen mu sun kokarin Karen kansu sosai anan ne aka kasha mutum 10, ‘yan bindigar ba sa saman abin hawa a kasa suke tafiya amma suna da yawa za su kai 100, a haka suka ci Karen ba babbaka suka wuce”.
Mahara sun addabi yankin Gwadabawa da Illela a kwanannan in da suke ta kai hari kan mai uwa da wabi a yankin, in da ko a satin nan sun yi garkuwa da mutum 16 a garin Gwadabawa in da har zuwa hada wannan rahoto ba a sake mutanen ba.
Shugaban karamar hukumar Illela Injiniya Aliyu Salihu ya ziyarci kauyen na Buwade domin ganin barnar da 'yan bindigar suka yi tare da jajantawa kan rasa maza 10 da aka yi da duba wadanda aka yi wa rauni da bayar da hakuri ga iyalan wadan da aka yi garkuwa da su.
Shugaban ya yi addu'ar samun zaman lafiya a yanki da ganin an sake daukar mataki domin kawo karshen matsalar a yankin.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Sakkwato Sanusi Abubakar bai daga kiran da aka yi masa domin sanin matakan da ake dauka a yankin.
managarciya