Gwamnatin Kebbi Ta Kaddamar Da Rabon Tallafin Kayan Abinci Na Naira Biliyan 5.7 Ga Mutanen Jiha

Gwamnatin Kebbi Ta Kaddamar Da Rabon Tallafin Kayan Abinci Na Naira Biliyan 5.7 Ga Mutanen Jiha
 

Daga Abbakar Aleeyu Anache 

 

A wannan juma'a ne Gwamnan Kebbi Dakta  Nasir Idris Kauran Gwandu ya jagoranci kaddamar da rabon tallafin rage radadin janye tallafin man fetur na kayan abinci ga al'ummar jihar kebbi da kudinsu yakai biliyan 5.7.

 
Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu ya bayyana cewa sun yi tanadi mai tarin yawa domin tallafawa mabukata in da babbar mota 210 suka dauko kayan abinci da kudinsu yakai sama da  biliyan biyar domin rabawa marasa karfi a jiha.
A wurin bukin kaddamarwar Gwamnan ya ce iyalai  dubu 550 ne za su amfana da tallafin.
"A kowace karamar hukuma daga cikin 21 za su karbi babbar mota 10 ta shinkafa da gero.
"Gwamnatin Kebbi ta kashe kudi sama da biliyan 5.7 don sayo kayan" a cewar Gwamna.