Matashi Zai Shafe Wata 6 Gidan Yari Kan Yiwa 'Yar Sanda Walakanci

Matashi Zai Shafe Wata 6 Gidan Yari Kan Yiwa 'Yar Sanda Walakanci
 

Wata kotun gargajiya mai daraja ta daya dake Ibadan jihar Oyo, a ranar Litinin ta yankewa matashi mai shekaru 23 mai suna Abayomi Damilare hukuncin zaman gidan maza na wata shida bayan ya watsawa ‘yar sanda kashi(najasa). 

Alkalin kotun ta yankewa matashin wannan hukuncin bayan ya amsa laifinsa tare da shaidu gamsassu da aka mikawa kotun.
Akintayo a takaice ta yi shari’a tare da yankewa matashin hukuncin wata shida a gidan yari da aiki mai wahala. 
Alkalin ta kwatanta wanda ta yankewa hukuncin da mai laifin da ba zai taba tuba ba, Daily Nigerian ta rahoto. 
Kamar yadda tace, wanda ta yankewa hukuncin an taba yanke masa hukuncin wata daya na bautawa al’umma kan wani mugun illa da yayi wa wani. 
Tun farko, ‘dan sanda mai gabatar da kara, Sajan Ayodele Ayeni, ya sanar da kotun cewa tun a caji ofis aka kulle shi kan zargin cin zarafin wata tsohuwa. Ayeni ya sanar da kotun cewa, Sajan Olofintuyi wacce ‘yar sanda ce ta hanzarta kai wa matashin dauki yayin da yake garkame. 
Kamar yadda yace, yana son ganawa da ‘dan sandan dake binciken lamarin. “Mai shari’a, Damilare ya dinga buga get din inda aka kulle shi yana son ganin IPO dake kula da lamarin yayin da Olofintuyi ta same shi. 
“Sai dai Damilare ya watsa nmata kashi tana bude inda yake kulle."  
Mai gabatar da kara yace Dan sandan ya mika hoton lokacin da cin zarafin ya faru da kuma takardar amsa laifinsa da yayi. 
Ayeni yace laifin ya ci karo da sashi na 356 na laifukan jihar Oyo a Najeriya na 2000.