Jinin Sojan Da Ya Kashe Abokin Aikinsa  Ya Kuma Kashe Kansa a Sakkwato Ba Zai Tafi a Banza Ba----Hukumar Soji

Jinin Sojan Da Ya Kashe Abokin Aikinsa  Ya Kuma Kashe Kansa a Sakkwato Ba Zai Tafi a Banza Ba----Hukumar Soji

 

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce za ta kaddamar da bincike kan wani jami'inta da ya bindige dan uwansa soja kana shi ma ya bindige kansa a wani sansanin sojoji dake karamarhukumar Rabah a Jihar Sokoto.

VOA ya rawaito cewa kakakin rundunar sojin, Janar Clement Nwachukwu, cikin wata sanarwa da ya sanya wa hanu, ya ce wannan abin bakin ciki dai ya faru ne ranar biyar ga wannan wata na Maris yayin da aka tura dakarun wani aikin tsaro.

Kawo yanzu dai rundunar ta ce bata san me ya sabbaba wannan ta'asar ba tunda sojin da ya harbe abokin aikin nasa shi ma ya bindige kansa daga bisani.

Tuni dai babban kwamandan runduna ta takwas dake birnin Sokoto wanda kuma shi ne kwamandan dakarun dake yaki da ‘yan bindiga dadi a arewa maso yamma wato OPERATION HADARIN DAJI Manjo Janar Godwin Makmut da sauran manyan sojoji suka ziyarci wurin da abin ya faru.

Bayan nuna rashin jin dadinsa, Janar Makmut ya hori sojojin da su  kasance ‘yan uwan juna kana su sa ido don kai rahoton duk wani abin da basu gane ba, don kaucewa aukuwar irin haka nan gaba.

Rundunar sojin Najeriya ta ce lalle ba ta ji dadin abin da ya faru bakuma abin ya dameta, dalilin kenan ma da ya sa aka kafa kwamitin bincike don gano ainihin abin da yasa hakan ya faru

Wannan dai ba shi ne karo na farko da soji ke kashe kansa a wuraren da mayakan ke fafatawa da ‘yan bindiga ko yan ta'adda ba.