Dokar haraji: Tinubu na shirin jefa Nijeriya cikin rikici: Gwamnan Bauchi
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce dokokin haraji da ke gaban majalisun taraiya, an kirkiro su ne don azurfa wani ɓangare na Nijeriya.
Daily Trust ta rawaito cewa da ya ke jawabi yayin da ya karbi wasu kiristoci da su ka kawo masa ziyara a gidan gwamnti na Bauchi, Mohammed ya gargadi shugaban kasa Bola Tinubu da ya janye batun dokokin haraji, yana mai cewa hakan na iya jefa ƙasa cikin rikici.
A cewarsa, wannan sabon tsarin ba zai amfani Arewa ba ko kadan, kuma yana iya hana gwamnoni damar biyan albashi.
managarciya