Sanata Lamiɗo ya jajantawa mutanen da suka yi hasara a ambaliyar ruwa a Gada

Sanata Lamiɗo ya jajantawa mutanen da suka yi hasara a ambaliyar ruwa a Gada
Dan majalisar dattijan Nijeriya dake wakiltan Gabascin Sakkwato Sanata Ibrahim Lamiɗo ya jajantawa mutanen Ɗantudu, Balaƙozo, Gidan-tudu da Tsitse dukkansu a ƙaramar hukumar Gada bayan da ambaliyar ruwa ta shafi yankunansu.
Sanata Lamiɗo a hirarsa da manema labarai ya aika saƙon jajensa ga al'ummar da suka samu jarabawar a ranar Laraba data gabata.
Ambaliyar ta shafi mutane 1,664 da yawan mutane sun bar gidajensu saboda rushewar gina da aka samu, an yi hasarar dabbobi da abinci.
Ambaliyar ta mamaye gona da yawa a ƙalla zai kai kadada 779.
Sanata Lamiɗo bayan jajanta masu ya ce zai yi wani da zai sa gwamnatin tarayya ta shigo domin tallafawa wadanda lamarin ya shafa ba tare da ɓata lokaci ba.