Gwamnatin jihar Lagos za ta kaddamar da karbar haraji yayin ajiye ababan hawa a wuraren ibada.
Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa dokar za ta fara aiki ne a watan Oktoban wannan shekara ta 2024 da muke ciki.
Shugaban sashen ayyuka na hukumar adana ababan hawa (LASPA), Ayokunle Akinrimisi shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da Vanguard ta samu.
Akinrimisi ya ce za a fara karbar harajin ne kowace awa da aka ajiye abun hawan a kan tituna da kuma wuraren ibada.
Har ila yau, ya ce za a dauki tsauraran matakai kan wadanda ke ajiye ababawan hawa ba bisa ka'ida ba a kan hanyoyi.
"Ina mai sanar da ku cewa hukumarmu za ta fara kawo sauyi game da ajiye ababan hawa a kan hanyoyin birnin Lagos."
"Ababan hawa da aka ajiye a coci-coci za su fara biyan kudi kowane awa kuma duk wadanda ke saba ka'aida za su fuskanci hukunci."
Hukumar ta kuma gargadi jama'a da su tabbatar sun bi dokar da aka gindaya wurin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Sai dai kuma hukumar ba ta bayyana yawan kudin da za a rika biya ba bayan ajiye ababan hawan a cikin birnin.