Sakataren gwamnatin jihar Bauchi ya ajiye aiki
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, ya amince da murabus din Sakataren Gwamnatin Jihar, Barista Ibrahim Muhammad Kashim
Wata sanarwa da mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin watsa labarai, Mukhtar M. Gidado, ya fitar ta bayyana cewa murabus din ya fara aiki nan take.
A cewar sanarwar, an umurci Shugaban Ma’aikata na Fadar Gwamnati, Dr. Aminu Hassan Gamawa, da ya karbi ragamar aikin Barista Kashim a matsayi na rikon kwarya.
Gwamna Bala ya gode wa Barista Kashim bisa ayyukan da ya gudanar wa jihar a lokacin da yake matsayin Sakataren Gwamnati .
managarciya