Sanata Barau zai ba da tallafin karatun digiri na biyu ga ɗalibai 300 ƴan asalin Kano

Sanata Barau zai ba da tallafin karatun digiri na biyu ga ɗalibai 300 ƴan asalin Kano

Mako guda bayan daukar nauyin dalibai 70 zuwa kasashen waje don karatun digiri na biyu,  Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya shirya ba da tallafin karatu ga dalibai 300 don karatun digiri na biyu a jami’o’in Najeriya.

Ƙarƙashin gidauniyar Barau I Jibrin (BIJF), an zabi ɗalibai 70 daga kananan hukumomi na jihar Kano, kuma sun tashi daga Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano zuwa Indiya a ranar 29 ga Disamba, 2024.

A jiya Litinin kuma , Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, wanda kuma shine Mataimakin Kakakin Majalisar ECOWAS, ya sanar da cewa ɗalibai 300 za su amfana daga shirin tallafin karatun digiri na gida da zai fara wannan shekarar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun sanatan, Ismail Mudashir, ya fitar, an bayyana cewa cibiyar ta buɗe neman tallafin karatun digirin  na cikin gida don shekarar karatu ta 2025/2026.

Sakataren Kwamitin Tallafin Karatu na gidauniyar, Maikudi Lawan, ya ce wannan shiri wata dama ce ta musamman don haɓaka ilimi, bincike, da ci gaban ɗan adam a fannoni daban-daban na kimiyya da fasaha, wanda zai bai wa matasa damar taka rawa wajen ci gaban ƙasa.

Ya ce an buɗe tallafin karatu a kan M.Sc. Artificial Intelligence, M.Sc. Robotics Technology, M.Sc. Cyber Security, M.Sc. Data Science, M.Sc. Information Technology, M.Sc. Software Development, M.Sc. Mineral Exploration, M.Sc. Hydrogeology & Environmental Geology, M.Sc. Oil and Gas Operations, M.Sc. Applied Geophysics, M.Sc. Metallurgical and Material Engineering, M.Sc. Climate Change Management, M.Eng. Mechatronic, da M.Eng. Intelligence System.

Ya ƙara da cewa an zaɓi jami’o’i shida don shirin, da su ka hada da Jami’ar Bayero Kano, Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, Jami’ar Ibadan, Jami’ar Legas, Jami’ar Obafemi Awolowo Ile-Ife, da Jami’ar Najeriya Nsukka.