Rage Karfin Ikon Sarkin Musulmi: Sakkwatawa Sun Yi Wa Gwamnati Barazana

Rage Karfin Ikon Sarkin Musulmi: Sakkwatawa Sun Yi Wa Gwamnati Barazana

Kwamishinan shari'a na jihar Sakkwato Muhammad Nasiru Binji ya ce Sarkin musulmi ba ya da hurumin da zai nada hakimai da uwayen kasa ba shi damar ya sabawa tsarin dokar kasa hakan ya sa ake son a yi gyaran kuskuren.

"Sashe na 76(2) a dokar kananan hukumomi da sarakuna ta baiwa Sarkin musulmi karfin ikon ya nada uwayen kasa da hakimmai a jiha bisa ga amincewar gwamna mai ci"

"Ba da wannan damar ya sabawa wannan sashen kan hakan ake bukatar a yi gyara."

Honarabul Shehu Kakale Shuni shugaban kungiyar Sakkwatawa mu koma tushe, ya ce "mu ba mu goyi bayan duk wani abu da zai kawo tarnaki ko rashin walwala ga Masarautar mai alfarma Sarkin musulmi ba, a takaice dai wannan kudirin doka ba mu goyon bayan shi, in har wani abu za a yi a karawa wannan majalisa karfi, ba wai a rage ba, Mai girma Sanata Wamakko shi ya yi wannan gyara kamar yadda magabata suka fada, hangen nesan da ya yi saboda darajar gidan ne, Sarautar Sarkin musulmi ba a Sakkwato ko Nijeriya kadai ba ce kowa ya sani, muna kira ga majalisa a yi amfani da idon basira a karawa majalisar mai alfarma Sarkin musulmi karfi ba ragewa ba."

Shehu Garbba Takatuku ya ce wannan sauraron jin  ra'ayin jama'a "hakika an  yi mana zalunci, abin da doka ta tanada a kira mutane a saurari ra'ayinsu  an kira mun zo ba a saurare mu ba."

Ya kalubalanci maganar kwamishinan shari'a ya ce bai fahimci yanda kundin tsarin doka yake magana ba, "amadadin kungiyarmu ta muhajiruna da lansaru ta dangin Mujaddadi Shehu Danfodiyo za mu dauki mataki, ba mu yarda da wannan dokar ba, za mu tafi kotu, kuma za mu yi amfani da kuri'armu tun da mu muka zabi wannan gwamnati, mu sauya ta a 2027." 

"Bai kamata gwamnonin Arewa suna cin zarafin sarakunanmu ba, bayan sun mayar da hankali ga harkar tsaro da tattalin arzikinmu amma sun koma duba wani abu daban na karbe aikin wasu, sarakuna ne ake jin maganarsu ake girmamawa, masarautar Sarkin musulmi cibiya ce ta addinin da al'adarmu, duk wanda ya ce ba zai yi da masarauta ba, ba za mu yarda ba," kalaman Alhaji Bandado Shehu, Magajin garin Silame.

Kwamared Kasim Na Kura shugaban kungiyar Matasan Arewa a Nijeriya ya a  matakin kungiyarmu ba mu yarda dokar da ake son a rage wa Sarkin musulmi karfin iko ba, muna son majalisa kar ta aminta da haka domin ragewa majalisa daraja da kima ne a idon jama'a.

Ya ce yakamata kwamishinan shari'a ya sani damar da ta ba da dama Gwamna ya nada Sarki ita ce ta ba da dama Sarki ya nada hakimmai da uwayen kasa, hakan bai sabawa doka ba domin gwamna na umartar wani yanada mukami a madadinsa.