Ganduje ya aikawa majalisa mutane da yake son a tantance bayan sun tafi hutu
Gwamna Ganduje ya aika wa majalisar dokokin Kano sunayen mutanen da za ta tantance
Daga Ibrahim Hamisu
Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya aika wa majalisar dokokin jihar sunayen shugabanni da kuma mambobin hukumar kula da ayyukan majalisar don tantancewa tare da tabbatar da su.
Hakan na cikin wata sanarwar da sakataren yaɗa labaran gwamnan Abba Anwar ya raba wa manema labarai a daren Larabar nan.
Mutanen da gwamnan ya aika da sunayen nasu, sun haɗa da Nasiru Mu’azu Kiru a matsayin Shugaban hukumar sai kuma mambobi 9 kamar haka:-
Ishaq Tanko Dala
Ali Abdu Doguwa
Salisu Abubakar Makoda
Isyaku Umar Mahmud Rurum
Ladan Sabo Ahmad Sumaila
Gambo Ibrahim Mai Wada
Ukashatu Bello Danbatta
Naziru Zakari Kumbotso
Sule Musa Adnan Warawa.
Sai dai gwamnan ya aika da takardar ne mai ɗauke da kwanan watan 31 ga watan da ya gabata na Agusta ne dai-dai lokacin da majalisar ta tafi hutun da ake sa ran za ta ci gaba da zama a ranar 13 ga wannan wata na Satumba da muke ciki.
managarciya