Sulhu Ne Maganin Rikice-rikicen Da Ake Fama Da Su----Janar Abdulsami Abubakar

Sulhu Ne Maganin Rikice-rikicen Da Ake Fama Da Su----Janar Abdulsami Abubakar

Sulhu Ne Maganin Rikice-rikicen Da Ake Fama Da Su----Janar Abdulsami Abubakar

 

Tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, ya bayyana cewar wajibi ne ƙasashen Afrika su canja salon yadda suke amfani da kokarin magance matsalar tsaro da  kawo zaman lafiya.

 
Abubakar ya bayyana haka ne a ranar Asabar a Abuja, yayin wani taro da aka gudanar domin karrama shi, inda ya ce "Yin amfani da ƙarfin soji ba zai kawo zaman lafiya da lumana ba."
 
"Har yanzu nahiyar Afirika tana fama da rikice-rikice iri daban-daban, waɗanda suna cikin manyan ƙalubalen da ke addabar nahiyar." Inji shi
 
Daga ƙarshe ya buƙaci shugabannin Afrika su rungumi sasantawa da yin sulhu wajen magance matsalolin rikice-rikicen dake addabar nahiyar.
Ana kallon matukar shugabanni a kasashe daban-daban suka yi da shawarar tsohon shugaban kasa ana iya samun sauyi a halin da ake ciki.