Abin Da Ke Damuwarmu Da Halin  Tambuwal------Bafarawa

Bafarawa ya ce yana godiya ga Gwamna Tambuwal da ya yarda su hadu a haka, kwalliya ta biya kudin sabulu domin abin da mutane ke son ji Tambuwal ya fara fado shi, akwai matsaloli da yawa wadanda ba matsala ba ne amma irin wannan zaman ne ya sa abin ya zama matsala. "ana son sanin mine ne gwamnati take ciki, shi kuma shugaba na son sanin mine ne mutane ke ciki, katse wannan ragar matsala za ta shiga, na ga wannan ragar tana son ta katse wanda in ta katse za mu shiga matsala," a cewar Bafarawa. Ya kawo wani misali kan abin da ya faru tsakaninsa da tsohon shugaban kasa Margayi Shehu Shagari ya ce "Allah ya gafartawa Shehu Shagari wata rana ya je ofishina ya ce gwamna kana aiki, amma akwai mutum biyu ka saurari daya kar ka saurari daya duk wanda yake yabonka ya ce kana aiki kar ka saurare shi

Abin Da Ke Damuwarmu Da Halin  Tambuwal------Bafarawa
Bafarawa
Tsohon gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bayyana abubuwan da suka zama karfe kafa tsakaninsu da gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal a wurin taron masu ruwa da tsaki na PDP da aka gudanar a satin da ya gabata, kamar yadda Managarciya ta samu bayani.
Bafarawa ya ce yana godiya ga Gwamna Tambuwal da ya yarda su hadu a haka, kwalliya ta biya kudin sabulu domin abin da mutane ke son ji Tambuwal ya fara fado shi, akwai matsaloli da yawa wadanda ba matsala ba ne amma irin wannan zaman ne ya sa abin ya zama matsala.
"ana son sanin mine ne gwamnati take ciki, shi kuma shugaba na son sanin mine ne mutane ke ciki, katse wannan ragar matsala za ta shiga, na ga wannan ragar tana son ta katse wanda in ta katse za mu shiga matsala," a cewar Bafarawa.
Ya kawo wani misali kan abin da ya faru tsakaninsa da tsohon shugaban kasa Margayi Shehu Shagari ya ce "Allah ya gafartawa Shehu Shagari wata rana ya je ofishina ya ce gwamna kana aiki, amma akwai mutum biyu ka saurari daya kar ka saurari daya duk wanda yake yabonka ya ce kana aiki kar ka saurare shi, amma ka saurari wanda zai soke ka in sukar tana da amfani shi ne masoyinka, mai yabonka zai kashe maka jiki, ba ka gane wannan sai ka bar kujera, aikinka zai sa a tuna da kai. Ina fatar mai girma gwamna ya hau wannan. A yanzu duk abin da za ka yi ba za a yaba ba, ba za a gode ba sai kabar wurin nan," Kalmomin Bafarawa.
Ya ce "Gwamna abin da ke damuwarmu da halinka sai kana ɓoye bayani ga talakawa gare mu ana kwaruwarmu da cuta mana, lokacin da nabar ofis ban ɓoye ba na bar kuɗi, kai ka zo ka gadi bashi, gwamna ko kana so ko baka so sai mun matsa mun samu record na gwamnatin data gabata. Gwamnatin Sakkwato  ba ta mutum daya ba ce duk tamu ce amma dole akwai shugaba," in ji Bafarawa.
Ya roki Tambuwal ya rika kula da malamai domin in malamai na addu'a Allah zai kawo sauki, akwai bukatar yin kwamitin malamai 'yan siyasa magoya bayan PDP.