Ban ga laifin jam'iyarmu ba don ta nemi Jonathan ya shigo cikinta-----Musa S/Adar
Ya ce APC da Jonathan suna yin wasar ɓera da mussa ne domin kowane yana auna nasara ko akasinta a cikin sabuwar dangantakar.
Ban ga laifin jam'iyarmu ba don ta nemi Jonathan ya shigo cikinta-----Musa S/Adar
Ɗan majalisar tarayyar Nijeriya da ke waƙiltar ƙananan hukumomin Gada da Goronyo a Sokoto Honorabul Musa Sarkin Adar ya fayyace biri har wutsiya kan ko APC za ta ba da takarar shugaban ƙasa a ɓangaren Kudu maso Gabas waton gefen da Igbo suka fi ƙarfi, da sauran bayanan jam'iya.
Honarabul S/Adar a hirarsa da gidan TV na Arise ya yi magana kan jitajitar da ake yaɗawa na cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya shirya shiga jam'iyar APC.
A cewarsa ba wani abu ba ne don jam'iyarsa na son tsohon shugaban ƙasar ya shigo cikinta. Ya ce "Wannan ake kira dimukuraɗiyya kuma Jonathan yana da damar ya yankewa kansa hukuncin abin da zai yi na shiga APC ko akasin haka.
Ya ce APC da Jonathan suna yin wasar ɓera da mussa ne domin kowane yana auna nasara ko akasinta a cikin sabuwar dangantakar.
Haka kuma jigon jam'iyar ya fito da wani abu da yake hasashen cewa tsohon shugaban ƙasar yana da damar da zai tsaya takarar shugaban ƙasa, amma siyasa abu ne na yawan jama'a ko an ba da takarar a Kudu, akwai wuyar gaske Kudu Maso Gabas ta iya samun tikitin takarar.
A cewarsa "Kudu maso yamma tafi yawan gwamnoni a yankin da suka fito a cikin jam'iyar APC. Duk wasu kiraye-kiraye da ake yi a Kudu ba su da matsala don akwai hakan a dimukuraɗiyya."
S/adar na ganin yawan masu ruwa da tsaki a jam'iyar APC daga kudu maso gabas zai sa yankin ya ji jiki kafin ya samu tikitin takara a jam'iyarsu.
managarciya