Obasanjo Ya Gana da Tsofaffin Shugaban Ƙasa Biyu A Neja, Ya Fadi Ba Ya Da Dan Takara Na Musamman a 2023

Obasanjo Ya Gana da Tsofaffin Shugaban Ƙasa Biyu A Neja, Ya Fadi Ba Ya Da Dan Takara Na Musamman a 2023

 

Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa ƙawancen da ya kulla da wasu yan takarar shugaban ƙasa ba yana nuna alamun yana da zaɓin ɗan takarar bane, kishin ƙasa ya sa a gaba. 

Vanguard ta ruwaito Dattijon ƙasan na cewa ba shi da wani ɗan takara da ya ke goyon bayan ko wata jam'iyya da yake so, amma ya sa kishin ƙasa a gaban komai.
Obasanjo ya yi wannan furucin ne a Minna, babban birnin jihar Neja bayan ya sa labule a lokuta daban-daban da tsoffin shugabannin ƙasa a mulkin soja, Janar Badamasi Babangida da Abdulsalami Abubakar ranar Lahadi. 
"Bani da wani ɗan takara na musamman a zaɓen shugaban kasa na 2023, amma ina da kishin ƙasa, ina da Ajenda ta ƙasa," Inji Obasanjo.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa a ƴan kwanakin nan, an ga Obasanjo ya gana da yan takarar shugaban kasa na jam'iyyu daban-daban kuma a lokuta mabanbanta.  
Tsohon shugaban ƙasa na tsawon zango biyu ya sa labule da Peter Obi na Labour Party, Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC da wasu fitattun ƴan siyasa a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito. 
Janar Abdulsalami da matarsa mai shari'a Fati Abubakar, sun rako tsohon shugaban har gaban Motarsa bayan kammala ganawar su da karfe 1:13 na rana. 
Daga nan, Obasanjo ya tafi zuwa gidan Janar Ibrahim Badamasi Babangida, inda anan ma suka gana da juna a sirrance.