Ganawar Tambuwal da Salame: Ziyara ko Zawarci?

Ganawar Tambuwal da Salame: Ziyara ko Zawarci?

Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Illele da Gwadabawa Honarabul Abdullahi Baalarabe Salame ya  ziyarci Gwamnan Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal a fadar gwamnatin jiha in da aka yi ganawar sirri tsakaninsu.

A zaman akwai shugaban jam’iyar PDP na  jiha Bello Aliyu Goronyo da dan takarar gwamna Alhaji Sa’idu Umar da Mukhtari Maigona, sai dai  bayan kammala ganawar ba a sanar da abin da aka tattauna ba, wasu jami’an gwamnati sun ce ziyara ce kawai ta sada zumunci.

Managarciya ta tuntubi Salame kan maganar ziyarar ya ce zumunci ya kai shi fadar ba neman wata takarar kujera ba.

“In mutum na son takara gidan gwamna yake zuwa yin takara, in ina son takarar dan majalisar tarayya da na yi tuntuni, ni ban ce ina son wata takara ba.

“Sannan zuwana gidan gwamna bashi ne na farko ba duk sanda akwai wasu abubuwa muhimmai ga kasa da jihar nan(Sakkwato), nakan tafi wurinsa, wannan zuwa ne na sada zumunci kamar yadda muka saba.

“Mun tattauna abubuwa muhimmai ga jihar nan kuma in Sha’Allah abubuwan da muka tattauna nan da sati daya za su fito fili,” a cewar Honarabul Salame.