DPO  Ya Lashe Musabaƙar Alƙurani Ta 'Yan Sanda A Kano

DPO  Ya Lashe Musabaƙar Alƙurani Ta 'Yan Sanda A Kano
DPO  Ya Lashe Musabaƙar Alƙurani Ta 'Yan Sanda A Kano
 
Shugaban Ofishin ‘Yan Sanda na Takai, DPO Mahi Ahmad Ali, shi ne ya zo na ɗaya a ajin izu 60, inda ya samu kyautar sabon firji da sauran kyaututtuka.
 
An kammala gasar karatun Alkur’ani mai girma da Rundunar ‘Yan sanda ta Jihar Kano ta shirya tsakanin jami’anta.
 
BBC Hausa ta rawaito Musabaƙar, wadda aka fara ranar Laraba, ta ƙunshi dakaru kuma mahaddata da suka fafata a matakin izu 60 da 40 da 5 da 2.
Wannan lamarin ya  faranta ran mutane da dama ganin yanda ake ƙara yi wa ƙur'ani hidima.
Musabaka abu ce mai kyau duk da wasu na ganin kamar ba ta da muhali a cikin harkokin addini.